Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)

Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)

-Yaro dan shekara 9 ne ke wakiltar Nigeria a gasar karatun Al Qur’ani a Algeria

-Dan takara Jabir ya ja hankalin jam’a saboda karancin shekarunsa na haihuwa

-Shi ne mafi karancin shekaru a cikin wadanda suka shiga gasar na duniya

Wani yaro dan Shekara 8 Jabir Abdullahi Abba ne ke wakiltar Najeriya a musabaqar al Qur’ai da ta kasa da kasa wacce ake yi gasar Tunisia.

Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)
Dan takara Jabir Abdullahi

A wani sako da Muhammad Abdullahi Abba wani dan uwan Jabir din ya lika a shafinsa na dandalin sada zumnta da muhawara na Facebook a intanet, ya ce Jabir ya shiga musabaqar ne a rukunin izifi 60 da kuma tajweed.

Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)
Jabir abdullahi da alkalan Musabaqa
Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)
Jabir Abdullahi da mahaifinsa Gwani Abdullahi a inda ake gudanar da Musabaqar a Algeria
Dan shekara 8 na wakiltar Nigeria a gasar Qur’ani (Hotuna)
Wani dan jarida na yi wa Jabir tambayoyi game takararsa

Dan takara gasar karatu Qur’ani mai wakiltar Najeria Jabir Abdullahi Abba, a cewar Muhammad Abba, dan uwan sa, ya haddace al Qur’ani mai girma ya na dan Shekara 8 da haihuwa, kuma ya  tafi kasar ta Aljeriyar ne domin halartar gasar ne tare rakiyar mahaifinsa Gwani Abdullahi Abba. Ana kuma sa ran Jabir zai taka rawar gani.

KU KARANTA: Ga matashin da ya rasa aikinsa saboda Boko Haram

Tuni dai ‘yan Najerya suka soma tofa albarkancin bakinsu dangane da wannan baiwa ta wakilci. Wanna dai ba shi ne karo na farko da Najeriya ke samun walkilci a gasar karatun Al Qur’ani mai girma a matakin kasa da kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel