DJ Cuppy: Rashin Miji Da Ɗa Abu Ne Mai Ciwo, Ɗiyar Attajirin Najeriya Femi Otedola

DJ Cuppy: Rashin Miji Da Ɗa Abu Ne Mai Ciwo, Ɗiyar Attajirin Najeriya Femi Otedola

  • Diyar hamshakin mai kudin Najeriya, Florence Otedola wacce aka fi sani da DJ Cuppy ta koka kan yadda take rayuwa babu aure ba magaji
  • A shafinta na X, DJ Cuppy ta ce 'abu ne mai muni' ace mace ta kai har shekaru 30 ba tare da aure ko samu haihuwa ba
  • A watan Disambar 2022 ne mawakiyar ta auri wani Ryan Taylor, sai dai auren bai juma ba suka rabu a watan Yulin 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shahararriyar DJ ta Najeriya, Florence Otedola, wacce aka fi sani da DJ Cuppy, ta ce a yanzu rashin aure ne yake yi mata illa a rayuwa.

A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, 'yar shekaru 31 ta ce zama mace marar aure da kuma rashin magaji a shekaru 30 abu ne 'mai munin gaske'.

Kara karanta wannan

Dalibi ya gwangwaje tsohon malaminsa da kyautar sabuwar mota da kudin mai na wata 12

Mawakiya DJ Cuppy ta koka kan rashin aure da haihuwa
Shahararriyar mawakiya DJ Cuppy, ta ce a yanzu rashin aure ne yake yi mata illa a rayuwa. Hoto: @cuppymusic
Asali: Twitter

DJ Cuppy, ta wallafa cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rayuwa babu aure kuma babu magaji ga mace mai shekara 30 abu ne mai munin gaske. Ba na yin komai sai abin da zuciyata ta raya mun, haka nake kullum."

Duba abin da ta rubuta a kasa:

DJ Cuppy ta taba yin aure amma ya mutu

Daily Trust ta tariyo cewa a watan Disambar 2022, mawakiyar ta Gelato ta yi aure da tsohon masoyinta, Ryan Taylor.

Sai dai kuma lamarin ya ba wa mutane da dama mamaki yayin da a watan Yulin shekarar da ta gabata ta sanar a kafar sadarwarta cewa ta rabu da Taylor.

Da take magana a wani taro na baya-bayan nan, DJ Cuppy wacce diyar attajirin dan kasuwa, Femi Otedola ce, ta ce duk da ita 'yar masu kudi ce, rayuwarta ta kasance "marar tabbas."

Kara karanta wannan

Mutane 5 wadanda suka fi karfin fada-aji a gwamnatin Buhari da yanzu aka daina jin duriyarsu

Cuppy ta kuma wallafa wani bidiyo inda ta tsaya tsakanin iyayenta, Femi da Nana Otedola, a wajen taron, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Matashiya ta sha alwashin auren hamshakin mai kudi

A wani labarin kuma, wata matashiya ta sha alwashin bin duk wata hanya da za ta iya bi don ganin ta auri hamshakin mai kudi.

A cewar matashiyar, iyayenta sun yi kuskuren auren juna alhalin sun san su duka talakawa ne, amma ita ba za ta yi irin wannan kuskuren ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel