Mawakiyar Najeriya DJ-Cuppy za ta yi wasan kalankuwa a kasar Saudiyya

Mawakiyar Najeriya DJ-Cuppy za ta yi wasan kalankuwa a kasar Saudiyya

Wata fitsararriyar mawakiya yar Najeriya, kuma diyar attajirin nan Femi Otedola, DJ Cuppy ta bayyana cewa za ta halarci kasar Saudiyya domin halartar bikin kalankuwa, inji rahoton The Cables.

Idan za’a tuna a kwanakin baya ne shahararriyar mawakiyar duniya, Nicki Minaj ta soke halartar zuwa kasar Saudiyya domin cashewa, inda ta danganta dalilin fasa halartar taron wakar ga tauye hakkokin mata da gwamnatin Saudiyya ta ke yi.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya roki Allah Ya saukar da masifa a kan masu keta alfarmar Al-Qur’ani

Cuppy ta sanar da niyyarta na halartar taron ne a shafinta na kasar sadarwar zamani ta Twitter, inda tace: ‘A matsayina na mace mai aikin sarrafa wakoki watau DJ, ina alfahari da gayyatar da aka min zuwa kasar Saudi Arabia domin na yi abin da na iya.

Har yanzu babu wani da ya yi ma Cuppy barazana, ba kamar a lokacin da Nicki Minaj ta yi shirin zuwa Saudiyya ba, wanda tace ta janye zuwa Saudiyyan ne domin bayyana goyon bayanta ga hakkokin mata da kuma hakkokin kungiyoyin yan luwadi, madigo, da masu sauya surarsu.

A wani labari kuma, Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya yi addu’ar Allah Ya saukar da fushinsa a kan duk masu cin mutuncin Al-Qur’ani a jahar Zamfara, sa’annan ya yi kira ga al’ummar jahar Zamfara dasu cigaba da rokon Allah a kan wannan matsala.

Matawalle ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 2 ga watan Disamba yayin bude taron gasar Al-Qur’ani mai girma na shekarar 2019 daya gudana a garin Gusau inda yace:

“Wannan addu’an ya zama wajibi saboda masu aikata laifin nan sun tafka mummunan badala wand aka iya janyo mana masifa, don haka haka muyi addu’a kada fushin Allah Ya shafemu.

“A matsayina na gwamna, na kafa kwamitin bincike, kuma duk wanda muka kama da laifi sai ya fuskanci hukunci kamar yadda dokokin shari’ar musulunci suka tanadar, duk girmansa kuwa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel