Duk Masu Zuwa Wurina Kudin Mahaifina Suke So Ba Ni Ba, Diyar Miloniya

Duk Masu Zuwa Wurina Kudin Mahaifina Suke So Ba Ni Ba, Diyar Miloniya

  • Dj Cuppy, diyar shahararren biloniyan nan na Najeriya, Femi Otedola ta magantu a kan dalilinta na rashin mallakar tsayayyen namiji
  • Matashiyar ta bayyana cewa duk masu zuwa wurinta ba soyayyarta ke kawo su ba illa kudin mahaifinta
  • Ta ce da zaran ta hadu da namiji magana na farko da ke fiotowa daga bakinsa shine yaushe zai hadu da mijinta

Shahararriyar mai hada sautin kida ta Najeriya, Florence Otedola, wacce aka fi sani da Dj Cuppy, ta magantu game da dalilin da yasa har yanzu bata da tsayayyen namiji.

Cuppy ta bayyana cewa yawancin mazan da ke shigowa rayuwarta ba sonta suke yi da gaskiya ba illa sai don kudin mahaifinta, Nigerian Tribune ta rahoto.

Otedola da Cuppy
Duk Masu Zuwa Wurina Kudin Mahaifina Suke So Ba Ni Ba, Diyar Miloniya Hoto: cuppymusic
Asali: Instagram

Matashiyar wacce ta kasance diyar shahararren dan kasuwa nan kuma biloniya, Femi Otedola, ba ta ce bata damu da hakan ba illa dai ta mayar da hankalinta wajen ganin mafarkinta ya zama gaskiya da kuma samun ilimi don zama irin macen da take sha’awa.

Kara karanta wannan

Attajira Ta Koma Titi Bara Bayan Kashe Dukiyarta Wajen Jinya Cututtuka

Budurwar wacce tayi karin haske game da shirinta na komawa makaranta don karantar fannin noma tace ba laifinta bane cewa maza na zuba ido a kan shaharar mahaifinta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta kara da cewa a duk lokacin da ta samu masoyi, tambaya na gaba da yake mata shine “yaushe zan hadu da mahaifinki?”

“Sai na tambayesu menene dalilin da yasa a kodayaushe suke magana game da mahaifina maimakon mayar da hankali a kaina da kuma abun da muke ciki. Ina mamakin dalilin da yasa duk suke mayar da hankali kan haduwa da mahaifina idan muna tattaunawa. Ina mamakin me yasa sunan mahaifina ke shigowa hirarmu.”

Kurma Ya ba Jama'a Mamakin Yadda Ya Tashi Mata 2 'Yan Gida Daya Kuma Yayi Wuff Da Su

A wani labarin, masu iya magana sun ce da dadin baki ake siye zukatan mata, amma wani mutumin kasar Rwanda wanda ya kasance kurma ya baiwa mutane da dama mamaki kan yadda ya shawo kan wasu mata biyu cikin sauki don su aure shi.

Kara karanta wannan

FG Zata Janye Rijistar Kungiyar ASUU, Ta Bayyana Dalilinta

Mutumin wanda bai tara dukiyar azo a gani ba ya fara auren Mabanti Maliya kuma Allah ya albarkacesu da yara uku.

Wata hira da Afrimax English ya bayyana cewa daya daga cikin yaran yayi mutuwar ban mamaki, amma sauran suna nan kuma babban cikinsu mai shekarunsa 20 yana rayuwa a wata uwa duniya. Dayan mai shekaru 19 yana nan a gaban iyayensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel