Ba Zan Maimaita Kuskuran Iyayena Ba, 'Yar Najeriya Ta Ci Alwashin Auren Attajiri

Ba Zan Maimaita Kuskuran Iyayena Ba, 'Yar Najeriya Ta Ci Alwashin Auren Attajiri

  • Wata matashiya 'yar Najeriya ta sha alwashin auren mai kudi ko ta halin kaka don gudun yin rayuwar talauci kamar yadda iyayenta suke ciki yanzu
  • Matashiyar ta ce ba za ta maimaita irin kuskuren da iyayen nata suka yi na auren junansu don soyayya ba, ga shi nan har yanzu ba su yi arzikin ba
  • Ta ce ma damar tana son samun kyakkyawar rayuwa nan gaba, dole ta nemo mai hannu da shuni, kuma ba za ta damu da wahalar da za ta sha ba.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Matashiya 'yar Najeriya da ke aikin podcast ta sha alwashin auren mai kudi ko ta halin kaka, a cewar ta ba za ta aikata kuskuren da iyayenta suka yi ba.

Kara karanta wannan

Kan ta waye: Yadda aka cinye kudi na da sunan za a yi min fim a Kannywood, Jaruma Saudat

Matashiyar mai suna Pearl, a shirin podcast na 'yan sama da shekaru 18, ta ce soyayya ba za ta rude ta wajen auren mutum don asalinsa ba, kudi kawai za ta bi.

Matashiya ta sha alwashin auren mai kudi
Matashiya 'yar Najeriya ta tayar da kura, ta sha alwashin auren mai kudi. Hoto: Twitter/@onejoblessboy
Asali: Twitter

Mahaifina talaka ne, dole in auri mai kudi - Pearl

A cewar tamahaifinta talaka ne, don haka ba za ta auri talaka ba, dole ta samu mai hannu da shuni don yin rayuwa cikin daula ko don gudun rayuwar wahala, Legit ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ta ke kare kanta, ta buga misali da attajiri Dangote wanda ta ce 'yayansa ba sa auren talakawa, tana nuni da cewa yanzu masu kudi sun fi son auren masu kudi.

Da wannan ta ke ganin ya zamar mata wajibi ta nemo mai kudi ko ta halin kaka tunda dai shi mahaifinta talaka ne, abin ba zai zo mata da sauki ba.

Kara karanta wannan

"Bana iya ajiye ko kwabo yanzu": Dan Najeriya da ke karbar N200k duk wata ya koka da tsadar rayuwa

Kalli bidiyon:

Sati daya da haduwarsu saurayi ya tura wa budurwa makudan kudade

A safiyar yau, muka kawo maku labarin wata matashiya wacce ta yi gamo da katar, inda saurayinta ya tura mata sama da dubu dari 700.

Matashiyar ta ce ko sati daya ba su yi da fara soyayya ba amma saurayin ke ta aika mata da kudi akai-akai, lamarin da ya jawo mutane suka taya ta murna.

Budurwa ta ce ba za ta iya auren mai daukar albashin N70K

A wani labarin, Legit ta kawo maku rahoton wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana irin ‘yan albashin da ba za ta iya aura ba a wani bidiyon da @kikiotolu ya yada.

Budurwar ta ce, ba za ta iya auren mutumin da ke samun N70,000 ba a wata. Ta kara da cewa, kudin sun yi kadan wajen kula da alakarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel