“Babu Miji, Babu ‘Da”: Budurwa Yar Shekaru 30 Ta Fashe Da Kuka a Bidiyo, Ta Bayyana Damuwarta

“Babu Miji, Babu ‘Da”: Budurwa Yar Shekaru 30 Ta Fashe Da Kuka a Bidiyo, Ta Bayyana Damuwarta

  • Bidiyon wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke sharban kuka da hawaye ya tsuma zukata a soshiyal midiya
  • Faifan bidiyon mai daidaita zuciya ya nuno matar tana kuka shabe-shabe yayin da take karin haske a kan abun da take fuskanta a rayuwa
  • A cewar matashiyar, bata yi aure ba har yanzu ko kuma mallakar 'da nata na kanta duk da cewar ta kai shekaru 30 a duniya

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta koka cike da dacin rai kan rashin aure yayin da ta kai shekaru 30 a duniya.

A cikin bidiyon da ta yada a shafinta na TikTok, matashiyar ta koka cewa har yanzu babu namijin da ya nemi aurenta a yawan shekaru irin nata.

Rayuwar kadaici ya ishi budurwa
“Babu Miji, Babu ‘Da”: Budurwa Yar Shekaru 30 Ta Fashe Da Kuka a Bidiyo, Ta Bayyana Damuwarta Hoto: @mediagist/Instagram.
Asali: Instagram

Budurwa ta koka saboda rashin aure a shekaru 30

Kara karanta wannan

Kannywood: Ali Nuhu Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Kara Aure Ba

Bidiyon TikTok din ya nuno ta tana sauraron wakar yabo yayin da take zubar da hawaye masu zafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamanta:

"Na dade ina sauraron wakarnan amma wannan ya taba ni sosai. Shekaru 30. Babu miji, babu 'da, babu iyali har yanzu", ta koka.

Jama'a sun yi martani kan bidiyon budurwar da ta koka saboda rashin aure a shekaru 30

@jecintainnocent ta rubuta:

"Toh ni na ce mai da nayi aure a shekaru 15 kuma na rasa mijina a shekaru 22 da yara 3."

@oyinkansola0430 ta yi martani:

"Yar'uwata zan cika shekaru 36 nan da yan kwanaki, babu da babu miji, ba mu muka halicci kanmu ba, akwai Allah."

@prettyedith21 ta ce:

"Yar'uwata shekaruna 34 babu 'da babu miji amma har yanzu na yarda cewa Allah na aiki a kan lamarina kuma zai yi mun zabin da ya dace ki daina kuka saboda lokaci bai kure ba tukuna."

Kara karanta wannan

"Kyau Iya Kyau": Bidiyon Jarumar Fim Da Biloniyan Mijinta a Wajen Bikin Diyar Sanata Sani Ya Girgiza Intanet

@kikelo19 ta yi martani:

"Ke yar'uwa nima shekaruna 30 babu miji babu 'da amma duk da haka na yarda cewa kwanan nan za mu ba da labari mai dadi don Allah ki daina kuka ina sonki."

Kalli bidiyon a kasa:

Amarya ta mutu a ranar aurenta a jihar Oyo

A wani labari na daban, mun ji cewa wata amarya mai suna Rebecca Oyedotun, ta yanke ciki ta fadi matacciya a ranar aurenta a yankin Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Mummunan al'amarin ya afku ne a jajiberin ranar aurenta yayin da ake bikin wankar amarya tare da kawayenta, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel