Wata Baiwar Allah Ta Rabu da Mijinta, Ta Zama Amaryar Saurayin ‘Diyarta a Kano

Wata Baiwar Allah Ta Rabu da Mijinta, Ta Zama Amaryar Saurayin ‘Diyarta a Kano

  • Malama Khadija Rano ta auri mutumin da ke neman a ba shi auren diyarta bayan abubuwa sun gagara
  • Wannan Baiwar Allah da ke Garin Rano ta ce diyarta ba ta sha’awar manemin, sai ita tayi wuf da shi
  • ‘Yanuwanta su na zargin Hisbah da daura wannan aure da ya jawo masu surutu ba tare da saninsu ba

Kano - Wani abin da ba a saba gani ba ya faru a garin Rano a jihar Kano, inda wata mata ta ruguza aurenta, ta auri wanda ake tunanin zai zama surukinta.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa wannan Baiwar Allah da aka bada sunanta a matsayin Malama Khadija, ta rabu da mijinta, sai ta auri saurayin ‘diyarta.

Abin ya faru ne bayan ita yarinyar mai suna Aisha ta nuna ba ta kaunar wannan mutum da ke neman ta da aure, sai uwar tayi amfani da wannan dama.

Kara karanta wannan

Mai Dakin Tinubu Za a Damkawa Mulki Idan Har Aka Zabi APC - Naja’atu Muhammad

‘Yanuwan matar sun shaidawa gidan rediyon Freedom su na zargin shugaban hukumar Hisbah na karamar hukumar Rano da daura aure ba da saninsu ba.

'Yan'uwa za su kai karar Hisbah

Rahoton ya nuna ‘yanuwan amaryar sun ce shugaban hisbah da ke garin Rano ya aurar da ‘yarsu ba da yardarsu ba, suka ce dole ne a binciki lamarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma da aka zanta da Malama Khadijah a gidan rediyon na Kano, ta shaida cewa tana nan lafiya kalau, kuma ta na zaune cikin zaman lafiya da angonta.

Wajen aure
Wurin bikin aure Hoto: EMAN EVENT CENTER LTD
Asali: Facebook

Khadijah take cewa bayan ta fahimci ‘yarta ba ta da niyyar auren wannan mutumi, sai ta ga bai kamata ayi asarar irinsa a dangi ba, sai ta tuntubi manyansa.

"Ni ma kyakkyawa ce"

Bugu da kari, Malama Khadijah ta ce yadda diyarta take da kyau, haka ita ma ta ke kyakkyawa.

Kara karanta wannan

Inda doka ke aiki: An ci tarar Firaministan wata kasa saboda bai sa bel a mota ba

Amaryar tayi amfani da ilmi ne domin kuwa ta ce sai da ta tuntubi malaman addini, kuma suka shaida mata hakan bai ci karo da addinin musulunci ba.

Abin da ya shigo da Hisbah

A lokacin da ta bijirowa manemin diyartan sai ya amince da maganar, amma ta ce iyaye da ‘yanuwanta suka ki bari a daura wannan aure haka kurum.

Ganin ba za ayi mata auren ba, matar ta je wajen hukumar Hisbah domin a biya mata bukata.

Malam Abdullahi Musa Rano wanda kawu ne a wajen matar, ya ce sun ki aurar da ita ga wannan mutum ne saboda da gan-gan ta kashe aurenta a dalilin shi.

An kai wa 'dan takara hari

An samu labari an aukawa Peter Obi da mutanensu a kan hanyarsu ta zuwa filin tashi da saukar jirgin sama. Hakan ya faru ne a lokacin da suka je Katsina.

Bayan nan, ‘yan iskan-gari sun rutsa tawagar ‘Dan takaran jam’iyyar LP da ruwan duwatsu. Kwamitin neman takaran LP ya bukaci jami’an tsaro suyi binciki.

Kara karanta wannan

ANgo ya Sanar da Mutuwar Amaryarsa Bayan Kwana 11 da Shan Shagalin Aurensu, Hotunan Bikinsu Sun Girgiza Zukatan Jama'a

Asali: Legit.ng

Online view pixel