Hotuna: Bayan Kwana 11 da Aure, Amarya Ta Amsa Kiran Mahaliccinta

Hotuna: Bayan Kwana 11 da Aure, Amarya Ta Amsa Kiran Mahaliccinta

  • Mutuwa tayi wa wasu sabbin ango da amarya yankan kauna bayan kwanaki 11 da shan shagalin aurensu inda ta dauke matar
  • Cike da alhini tare da karayar zuciya, ango mai suna Idris Almustapha Daja ya sanar da mutuwar kyakyawar matarsa tare da wallafa hotunansu
  • Tuni jama'a suka dinga tururuwar yi masa ta'aziyya tare da taya shi alhinin rashinta inda su ke masa fatan juriya da samun wacce ta fi ta

Mutuwa riga ce in ji Malama bahaushe kuma ba a iya cire ta. Wani anngo ya dandana daci da zafin mutuwar masoyiyarsa abar kaunarsa, kuma amaryarsa bayan kwanaki 11 kacal da yin aurensu.

Matashin angon mai suna Idris Almustapha Daja mai amfani da @almustapherr a shafinsa na Twitter, ya bayyana labarin mutuwar kyakyawar amaryarsa bayan kwana 11 da aurensu.

Kara karanta wannan

Bidiyon Baturiya Tana Yawo a Hargitse Babu Takalmi a Lagas Ya Girgiza Intanet, Bidiyon Ya Yadu

Amarya da Ango
Hotuna: Bayan Kwana 11 da Aure, Amarya Ta Amsa Kiran Mahaliccinta. Hoto daga @almustapherr
Asali: Twitter

Cike da alhini ya saka hotunansa na aure tare da matarsa inda yayi nadin sarauta yayin da marigayiyar ta saka alkyabba.

A hotunan, kai tsaye ka na iya gane cewa wannan auren soyayya ne duba da yadda suke ta murmushi mai nuna cewa dogon buri ne na masoya ya cika.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wallafarsa yace:

"Daga Allah mu ke, kuma gare shi za mu koma. Na rasa ta bayan kwanaki 11 da aurenmu. 6 ga watan Janairun 2023 zuwa 17 ga watan Janairun 2023."

Jama'a sun yi martani

Bayan wallafar nan babu dadewa, jama'a sun dinga tururuwar yi masa jaje da ta'aziyyar wannan rashin da yayi na masoyiyarsa.

Ga wasu daga cikin sharhin jama'a:

Engr Yasir Arafat Jubril yace:

"Allah ya gafarta mata. Allah ya ba ku hakurin Musulunci."

SALT tace:

"Oh Allah, Daga Allah mu ke kuma gare shi za mu koma. Allah yayi mata rahama Amin. Muna rokon Allah cikin rahamarsa ya saka ta a Aljanna. Alla ya ba mijinta abinda yafin alheri kuma ya bashi hakurin jure wannan rashin."

Kara karanta wannan

Budurwa Mai Yara Uku Kowane Mahaifinsa Daban Ta Fashe da Kuka a Bidiyo, Tace Aure Take So

Abu Muhammad yace:

"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Wannan lokacin takaici ne gare ka. Allah ya gafarta mata, ya ba ka karfin jure hakan kuma ya maye maka gurbinta da wata wacce ta fi ta ta kowacce fuska."

Fatteh Hamid yace:

"Allah ya karba bakuncinta kuma ina fatan ya saka ta a Aljanna madaukakiya."

Yasmin Umar tace:

"Daga Allah mu ke kuma gare shi za mu koma. Allah ya gafarta mata yasa aljanna makomarta. Allah ya ba ka hakurin rashin ta sannan ya musanya maka da mafi alheri."

Tijjani Muhammad yace:

"Na tausaya maka da wannan rashin na matar ka masoyiyar ka. Allah ya bata Aljannar Firdausi.

Iyayen amarya sun ki karbar sadaki saboda doya 1 cikin 400 ta karye

A wani labari na daban, wasu iyayen budurwa sun yi watsi da sadakin da aka kai na diyarsu bayan ganin doya daya tak karyayya cikin gida 400 da suka bukata.

Sun ce lallai masoyin diyarsu ya je ya siyo karin dayar nan don ba zasu karba karyayya doya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel