Latest
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun tursasa mutane zuwa cikin daji.
Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi magana kan matsayarsa a APC inda ya jaddada cewa har yanzu mamba ne na jam’iyyar kuma yana son a dinga kiransa haka.
Majalisar Wakilai ta amince da kudirorin haraji, ta soke bukatar karin VAT, ta samar da sabuwar Hukumar Haraji ta Najeriya, tare da kafa kotun korafe-korafen haraji.
Kungiyar shugabannin kananan hukumomi (ALGON) reshen jihar Kaduna, sun yabi salon mulkin Gwamna Uba Sani. Sun yi masa alkawarin goya masa baya a 2027.
Gwamna Bala ya ce yana shirye ya yi aiki da Peter Obi domin karfafa adawa a gabanin 2027, yayin da Obi ya jaddada cewa talauci ne tushen matsalar rashin tsaro.
Karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bi sahun masu yi wa Nasir Ahmad El-Rufai raddi kan sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya, Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam'iyyar SDP ta hadu da Nasir El-Rufa'i. Ya sauya sheka ne a Abuja.
Muƙaddashin shugabam PDP na kasa, Ambasada Umar Damagum ya bayyana cewa zaben da tsagin Wike suka shirya na shugabannin jam'iyya a Kudu maso Kudu ya saɓa doka.
Sabon rahoto ya nuna cewa tsohon shugaban kasar Nijar, Ibrahim Baré Maïnassara ne ya kafa rundunar Lakurawa a 1997 domin yaki da masu satar shanu.
Masu zafi
Samu kari