Latest
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan wani yunkurin kai harin ta'addanci da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar Adamawa. Sun fatattake su zuwa daji.
Bayan zargin cewa Bola Tinubu ke ɗaukar nauyin SDP, fadar shugaban kasa da jam'iyyar sun karyata jita-jitar da ake haɗawa da ba ga sa tushe bare makama.
Matatar Dangote ta sayi danyen man Ceiba har ganga 950,000 daga kasar Equatorial Guinea, yayin da NNPC ke tattaunawa da matatar kan tsarin sayen danyen mai da Naira.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yabawa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan tabbacin da ya bayar na ci gaba da kasancewarsa mamba a cikinta.
Jami’an tsaro sun dakile wani harin ‘yan bindiga a jihar Katsina, inda suka kashe dan ta'adda daya, sannan suka kwato makamai, babura da sauran kayan aikin miyagun.
Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Damagum, ya bayyana rahotannin da ake yadawa masu cewa ya yi murabus, a matsayin tsantsagwaron karya.
Bayan Nasir El-Rufai ya kira jiga-jigan PDP su koma SDP, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce ba shi da darajar shugabanci da zai iya janyo su.
Yayin da ake ci gaba da shari'a kan zargin samun makudan kudi a asusun Abba Kyari, Iyalansa sun karyata zargin yana da asusun banki guda 10 da N200m.
Aminu Babba Ɗan'agundi ya yi barazanar sake maka Muhammadu Sanusi II a gabam kotu idan har ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin sarkin masarautar Kano.
Masu zafi
Samu kari