Latest
Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram. Sojojin sun cafke mai kawo musu jirage marasa matuka.
Bincike ya bayyana dangantakar Jeffrey Epstein da Ehud Barak a harkar riba daga rikicin Boko Haram a Najeriya, tare da amfani da tashoshin jiragen ruwa da kan tsaro.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta takaita zirga zirga a jihar Kano a shirin zaben cike gibi da za a yi a karamar hukumar Birni da Ungogo a gobe Asabar.
Babban hafsan tsaron kasa (CDS), Janar Olufemi Olatubosun Oluyede, ya kaddamar da rundunar Operation Savannah Shield, da za ta fattaki 'yan ta'adda a Kwara Neja.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bai wa ƙasar Iran wa’adin kwanaki 10 zuwa 15 domin cimma yarjejeniya kan shirin nukiliyarta ko kuma su fuskanci matsala.
'Yan ta’adda sun tura wasika ga al’ummar Utono, Kebbi, suna neman N100m kafin su shiga gari domin “wa’azi”, yayin da gwamnati ta tura jami’an tsaro don kare su.
Rundunar 'yan sanda ta kama tsohon hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Okoi Obono-Obla kan zargin shiga aikin lauya ba bisa ka'ida ba a jihar Cross River.
A labarin nan, za a ji cewa an samu rahoton hukumar tsaron DSS ta fara shirin gayyatar wasu da ake zargi suna da masaniya a kan bacewar dan gwagwarmaya, Dadiyata.
An sake samun tashin gobara a wata fitacciyar kasuwa da ke jihar Kano. Gobarar dai ta tashi ne da asuba. Majiyoyi sun bayyana cewa gobarar ta lakume shaguna.
Masu zafi
Samu kari