Jarumin Kannywood, Sadik Sani Sadik Ya Fallasa Kansa, Ya Fadi Dalilin Shigarsa Fim
- Jarumin Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce ya na harkar fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, yana neman kuɗi ne kawai
- Matashin 'dan wasan kwaikwayon ya ce tarbiyya daga gida take fitowa yayin da ya ce malamai ke fadakarwa, ba 'yan fim ba
- Sadik Sani Sadik ya jaddada cewa idan fim dinsa ya shafi tarbiyya, laifin iyaye ne ba nasa ba saboda nauyi na kansu
- A cewarsa, mata da maza ba su da bambanci wajen samun kudi a masana'antar wasan fim, ya ce komai ya na da sirri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Sadik Sani Sadik, ya ce fim da yake yi ba wai don ya koyar da tarbiyya ba ne.
A cewarsa, kawai yana neman kuɗi ne, ba wai ya na kokarin koya wa mutane darussa ba.

Asali: UGC
Jarumi ya yi fatan fim ya kai shi aljanna
Wannan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo yayin wata hira da gidan rediyon Freedom da aka wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan shahararren jarumin Kannywood, Sadi Sani Sadiq ya yi wasu zantuka masu tsuma zukata kan sana'arsa ta fim.
Jarumin fim din ya ce yana fatan wannan sana'a tasa da yake yi za ta yi sanadiyar shigarsa gidan Aljannah.
Sadiq ya kuma bayyana cewa bai da ubangida a harkar fim amma akwai wasu da ya ke ganin girmansu matuka a masana'antar.
Sadik Sani Sadik ya magantu kan tarbiyya
Sadik ya ce yana son a fahimce shi bisa gaskiya cewa ba shi da wata alaka da tarbiyya a fim.
Ya ce:
“Ni ban ce ina fadakarwa ba, ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba, ban kuma ce ina tarbiyyantarwa ba.”
Ya ƙara da cewa iyaye da malamai ne ke da alhakin koyar da tarbiyya ga al'umma wanda ke farawa daga gida.
Jarumin ya bayyana cewa:
“Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi, ni ba mai fadakarwa ba ne, ni mai neman kudi ne.”

Asali: UGC
Sadik Sani Sadik ya fadi inda ake samun tarbiyya
Jarumin ya ce fim ba shi da addini ko harshe, komai ya danganta da yadda mutum ya gudanar da nashi aikin.
Dangane da sukar da ake yi wa wasu fina-finai na Hausa, Sadik ya ce:
“Idan danka ya kalli fim dina, tarbiyyarsa ta tabu, ba daga ni ba ne, daga kai ne.”
Sadik ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu ke ganin kallon fim na Hausa da dan taba mace ya zama babban al’amari.
Da aka tambaye shi batun cewa mata sun fi maza kudi a yanzu, Sadik ya bayyana ra’ayinsa da cewa hakan ya danganta da yanayin mace kuma komai ya na da sirri.

Kara karanta wannan
Tirkashi: Lauyoyin Najeriya sun kawo dokokin da suka hana Tinubu dakatar da Fubara
Baba Rabe ya shawarci malamai kan harkar fim
Kun ji cewa sanannen jarumin Kannywood, Abubakar Waziri ya ce da ba ya harkar fim, da watakila ya zama malamin addini saboda yana da sha’awar gyaran tarbiyya.
Jarumin da aka fi sani da Baba Rabe ya bukaci malamai su shiga harkar fim domin yawancin jama’a yanzu suna kallon fim fiye da sauraron wa’azi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng