Jerin fina-finan Kannywood 5 da suka yi tashe a shekarar 2021

Jerin fina-finan Kannywood 5 da suka yi tashe a shekarar 2021

A yayin da shekarar 2021 ke zuwa karshe, ya dace mu tuna da wasu abubuwan da suka faru a cikin shekarar. Masana'antar Kannywood ta fitar da fina-finai daban-daban wadanda suka dauka hankalin masu kallo matuka.

Hakazalika, wasu fina-finan sun yi shuhura a wannan shekarar inda masu kallo suka dinga kwasar nishadi da jin dadi yayin kallonsu, lamarin da yasa suka yi matukar tashe a shekarar nan.

Jerin fina-finan Kannywood 5 da suka yi tashe a shekarar 2021
Jerin fina-finan Kannywood 5 da suka yi tashe a shekarar 2021. Hotuna daga @manasurahisah, @yusuf_saseen, @lawanahmed@nafeesatabdullahi
Asali: Instagram

Legit.ng ta tattaro muku wasu jerin fina-finai 5 da suka yi matukar tashe a cikin shekarar 2021.

1. Labarina

Babu shakka fim din Labarina ya yi matukar tashe a cikin shekarar nan. Abubuwa masu yawa sun ja hankalin masu kallo zuwa kallon fim din mai dogon zango.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kannywood: Dalilin da yasa muka maida fina-finan Hausa kan Youtube, Ali Nuhu

Daga cikin abubuwan da suka ja hankalin mutane kuwa akwai soyayya, halasci, cin amana, hakuri da kuma sakayya duk da aka gani a cikin fim din.

2. Izzar so

Wannan shiri ne mai dogon zango wanda jarumi Lawan Ahmad ya shirya shi kuma ake sakinsa a kowanne mako.

Wannan shirin ya ja hankalin mutane saboda ya dauko sabbin 'yan wasa wadanda suka matukar taka rawar gani wurin wasan kwaikwayon.

3. Fanan

Babu shakka fim din Fanan ya dauka hankali jama'a masu tarin yawa. Tun kafin fitar fim din a sinima, an dinga tallarsa kuma wakar da ke ciki ta matukar kayatar da jama'a.

Wannan fim din na tsohuwar jaruma Mansurah Isah ne inda tsohon mijinta tare da diyarta Iman Sani Danja suka bayyana.

4. Gidan Badamasi

Wannan shirin mai dogon zango ya ja hankalin masu kallo duk da kuwa ba wannan shekarar aka fara yin sa ba.

Dalilin kuwa da yasa hankalin jama'a ya karkata kan wannan fim din shi ne sabbin 'yan wasa da aka kara a ciki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba

5. Kwana Casa'in

Shirin kwana casa'in shiri ne mai dogon zango mai cike da 'yan wasa tsofaffi da kuma masu tasowa.

Akalar shirin ta karkata ne kan yanayin tsarin shugabanci, siyasa da kuma yaki da rashawa. Tabbas masu kallo suna daukin wannan fim da ake fitarwa a kowanne mako.

Jaruman Kannywood 12 da Taurarinsu suka fi haskawa a 2021

A wani labari na daban, masana'antar Kannywood dai na kunshe ne da jarumai masu tarin yawa. Akwai tsoffin jarumai, sabbi da kuma masu tasowa. Wasu sun yi suna ne a wannan shekarar sakamakon rawar da suke takawa a wasu fina-finai masu dogon zango.

A cikin shekarar nan ta 2021, akwai jaruman da tauraruwarsu ta fi haskawa sakamakon wata rawa da suka taka a wasu sabbin fina-finai ko kuma makamancin hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel