Allah ya yi wa jarumin Kannywood Ubale Ibrahim rasuwa
Allah ya yi wa daya daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Ubale Ibrahim wanda aka fi sani da wanke wanke rasuwa.
Jarumin ya rasu ne a daren ranar Alhamis, 30 ga watan Afrilu.
Za a yi jana’izar marigayin a yau Juma’a, 1 ga watan Mayu, da karfe 8:00 na safe a Rangaza bayan gidan man Chalawa, kamar yadda jarumi Sani Danja ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Mutuwar Ubale na zuwa ne a daidailokacin da ake tsaka da yawan mace-mace na ban mamaki a jahar Kano.
Tuni dai yan uwansa jarumai na masana’antar fim suka fara nuna alhini da yi masa addu’a a shafin Instagram.
Ga wasu daga cikin jaruman da suka yi ta'aziyyar marigayin:
Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa: “Allah ya jikan Ubale Ibrahim, ya sa mutuwa hutu ce gareshi.”
Falalu A Dorayi ya wallafa a nasa shafin: “Innalillahi wainna ilaihi rajiun. Allah yayi wa UBALE IBRAHIM (wanke-wanke) Rasuwa. Yan uwa mu sanya shi a addua. Allah yai masa rahma.”
Nuhu Abdullahi: “Allah ya gafarta maka Ubale, YA kuma yafe maka kura-kuran ka, YA sa aljannace makomar ka, amin.”
Fati Abubakar: “Innalillahi wa'inna ilaihiraju'un Allah ya gafarta maka kura kuranka amin”
A gefe guda mun ji cewa jama'ar Kano na zaune cikin fargaba saboda yawaitar mace - macen mutane, yawancinsu tsoffi, da ake samau a cikin birnin jihar.
Tun a makon jiya gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya saka dokar kulle jihar Kano; ba shiga, ba fita, sannan jama'a ma ba za su fito daga gidajensu ba. Gwamnatin jihar ta dauki wannan tsatsauran mataki ne biyo bayan bullar annobar covid-19 a jihar.
Duk da gwamnatin Kano ta musanta labarin yawaitar mutuwar mutane a cikin birnin jihar, rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da ke mutuwa ya na cigaba da karuwa.
An samu mutuwar mutane da dama a cikin birnin Kano da kewaye daga yammacin ranar Juma'a zuwa ranar Asabar da rana.
Fitattu daga cikin wadanda su ka mutu akwai: tsohon kwamishina a jihar Kano; Farfesa Ibrahim Ayagi, editan jaridar Triump; Musa Ahmad Tijjani, tsohon shugaban hukumar ma'aikatan jihar Kano; Adamu Dal.
Sauran sune: Nasiru Maikano Bichi, Musa Umar Gwarzo, Ustaz Dahiru Rabi'u, tsohon alkali; Khadi Salisu Lado, Nene Umma, Garba Sarki Fagge, Salisu Lado, Shamsiyya Mustapha, Nene Umma, Garba Sarki Fagge, Rabiu Dambatta, Kabiru Ibrahim Bayero da mahaifiyar fitaccen mawaki, Ado Gwanja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng