'Yan Ta'adda Za Su Buɗe Sabon Gidan Rediyo Na Musamman a Najeriya, an Gano Dalili
- Yayin da Najeriya ke cikin mawuyacin halin rashin tsaro, kungiyar ISWAP ta shirya bude sabon gidan rediyo a kasar
- ISWAP ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude gidan rediyon yanar gizo a kokarin ci gaba da yada manufofinta
- Wannan na zuwa ne yayin da sojoji ke kokarin dakile matsalolin tsaro a ɓangarorin kasar baki daya domin samun zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - Kungiyar ISWAP ta kammala dukkan shirye-shirye domin bude sabon gidan rediyo na musamman.
Kungiyar ta shirya bude gidan rediyon ne a yanar gizo mai suna "Radio Raeed" domin yaɗa manufofinta.
Musabbabin bude sabon gidan rediyon
ISWAP ta ce za ta yi amfani da gidan rediyon domin shawo kan jama'a shiga kungiyar musamman a yankin Arewa maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zagazola Makama ta tattaro cewa gidan rediyon zai kasance a Kangarwa wanda zai ba da karfi wurin kafa shari'ar Musulunci a yankin.
Har ila yaushe, za a rinka gabatar da shirye-shirye a cikin harsunan Hausa da Larabci da kuma Kanuri.
Wannan mataki na kungiyar ya kara tabbatar da yadda suke samun ƙarfi musamman a Arewa maso Gabas, cewar Daily Post.
Sojoji sun gargadi 'yan ta'adda
Har ila yau, Babban hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja ya sha alwashin cewa rundunar sojoji ba za ta saurara ba har sai ta ga bayan ƴan ta'adda.
Lagbaja ya kuma ja kunnen masu aikata laifuka da sauran masu son kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasar nan da su shiga taitayinsu ko su fuskanci hukunci.
Yan bindiga sun kashe sojoji 6
A wani labarin, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi ajalin jami'an sojoji akalla shida a wani mummunan hari a jihar Neja.
Yayin harin da ya yi ajalin sojojin, maharan sun kuma yi garkuwa da wani Kyaftin din sojoji inda suka tsere da shi ba tare da sanin inda suka yi ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da 'yan bindiga ke yin ajalin sojoji wadanda al'umma suka dogara da su domin dakile matsalar tsaro a kasar.
Asali: Legit.ng