Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood

Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood

  • Jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Auwal Isah West ya caccaki abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon kan wasu manyan masana'antar
  • Gabon dai ta yi hannunka mai sanda ga wasu manyan jaruman masana'antar, inda ta zarge su da yiwa whitemoney wanda ya lashe gasar BBNaija shishigi
  • Sai dai West ya mayar mata da martani, inda ya ce ta yi butulci ga wadanda suka daukaka ta har duniya ta santa

Kano - Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Auwal Isah West ya caccaki abokiyar sana’arsa, Hadiza Gabon bayan tayi hannunka mai sanda ga wasunsu da suka halarci taro da kamfanin multichoice ta shirya.

Kamfanin dai ya shirya taron liytafar ne na karrama ‘wadanda suka lashe gasar BBNaija a garin Kano, inda manyan jarumai irin su Ali Nuhu, Rasheeda mai Sa’a, darakta Bashir Mai Shadda, Naziru Danhajiya da sauransu suka halarta.

Read also

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood
Bidiyon Auwal West yana caccakar Hadiza Gabon kan hannunka mai sanda da tayi wa wasu manyan Kannywood Hoto: allin-one.com
Source: UGC

Sai dai kuma, Jaruma Hadiza Gabon ta caccaki abokan sana'arta da yiwa whitemoney wanda ya lashe gasar shishigi. Sannan tace duk rawar jikin da suka dunga yi bai daura su a shafinsa na sosjhiyal midiya ba.

Wannan abu ya harzuka Auwal West inda ya fito ya mayar mata da martini tare da zarginta da yi wa wadanda suka daukaka ta butulci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin bidiyon da shafin jakadiyan_arewa_tv ta wallafa an jiyo West yana cewa:

“Hadiza da kike magana kike cewa da haka ake daga namu, ki gaya mana wani jarumi na Kannywood mace ko namiji wanda abun farin ciki ko bakin ciki ya same shi da ba a posting din shi ko an taya shi jaje ko farin ciki ba.
“Ke da kike wannan maganar rashin sanin girman naga ba da ke ne da wadanda suka taimaki rayuwarki da Allah ya taimake ki. Kada ki manta lokacin da Yakubu Lere ya turo Jamilu Kochila ya kowo ki daga Kaduna zuwa Jos zaki yi fim ko Hausa ba kya ji, daya daga wadannan da kike magana a kansu daya daga cikin wadanda kika ce basa daga naku shine ya saka ki a fim sannan wasu suka gan ki suka saka ki fim, Allah ya daga ki duniya ta san ki amma yau har kike Magana saboda raini.

Read also

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Maulidi a Najeriya

“Amma saboda wasunku butulu ne ku idan kuka ci kuka koshi kuka zauna iskar AC ya fara buga ku sai ku manta da alkhairi. Shima kawalinku da ke mara maku baya na Abuja wanda muka kasa gane gabansa Musulmi ne shi ko akasin haka mun ga rainin naku ya fara yawa dole mu tuna maku baya.
“Mutanen da kike Magana a kai ba wai sun je suka samu Whitemoney suka yi hoto da su ba sune suka zo suka same su domin mutane ne masu daraja masu kima.”

Ga bidiyon a kasa:

Ana yi wa ‘yan Kannywood shaidar kin zaman aure alhalin kaddara ce ke fito da su – Maryam Malika

A wani labarin, shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Muhammad wacce ake yiwa inkiya da Maryam Malika ta yi martani a kan yadda mutane ke yi wa jarumai mata shaidar kin zaman aure.

Read also

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa da kujerun da suka nema

A wata hira da aka yi da jarumar a shirin ‘Daga bakin mai ita’ wanda sashen Hausa na BBC ke gudanarwa, ta jadadda cewa burin kowace yarinya da iyayenta shine ganinta a dakin aurenta.

Malika wacce ta bayyana rashin jin dadinta a kan wannan bakin fenti da ake shafa masu, ta kuma bayyana cewa kaddara ce ke rabo su da dakin mijinsu wanda mutane kan manta hakan.

Source: Legit

Online view pixel