Rahama Sadau Ta Bayyana Cewa Ba Da Gan-Gan Ta Ke Abubuwan Da Ke Jawo Cece-Kuce Ba

Rahama Sadau Ta Bayyana Cewa Ba Da Gan-Gan Ta Ke Abubuwan Da Ke Jawo Cece-Kuce Ba

  • Shahararriyar jarumar fina-finai, Rahama Sadau ta yi martani kan cece-kucen da ta ke jawo wa
  • Sadau ta ce mutane ba su fahimce ta ba, mafi yawan abin da ke jawo cece-kucen ba da nufi ta ke yi ba aiki ne ke jawo wa
  • Ta bayyana cewa ba ta taba dana-sanin hakan ba kawai a kullum ya na zama mata darasi ne a rayuwarta

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Jarumar fina-finai, Rahama Sadau ta bayyana yadda mutane su ka sakata a gaba duk lokacin da ta yi wani abu.

Sadau ta ce akwai taurari da dama da su ke abin da ya fi nata, amma jira ake ta yi wanda bai kai nasu na sai ayi ta cece-kuce.

Rahama Sadau ta yi martani kan cece-kucen da ta ke jawo wa
Rahama Sadau Ta Magantu Kan Cece-Kuce Da Ake A Kanta. Hoto: rahamasadau.
Asali: UGC

Me ye Rahama Sadau ke cewa kan cece-kucen?

Jarumar ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo yayin da TRT Hausa ke hira da ita a yau Litinin 11 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wata Mata Ta Faɗi Ta Mutu a Kan Gada Cikin Yanayi Mai Ban Tausayi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ce kaso 90 na abubuwan da ke jawo cece-kuce a kanta ba ta taba yi don ayi magana ba ko dan ta yi suna.

Sadau ta ce akwai dabi'a da take da shi a rayuwarta wanda ba lallai ya yi wa wasu dadi ba.

Ta kara da cewa ya danganta saboda kowa da irin shahararsa a wasan kwaikwayo ko wani bangare daban.

Rahama Sadau ta ce ba ta dana sanin aikata hakan

A cewarta:

"Kaso 90 na abubuwan da ke jawo cece-kuce ba ina yi ne don ayi magana ba, kawai dabi'a ce wacce ke taka rawa a rayuwata.
"Akwai jarumai daza su yi abin da ya fi nawa, amma ba a magana, idan ni na yi wanda bai kai na su ba, sai ka ji ana Rahama ta yi kaza, Rahama ta yi kaza.

Kara karanta wannan

Yadda Binciken Da Tinubu Yake Yi Zai Tona Barnar da Buhari Ya Yi – Kanal Dangiwa

"Ban taba dana-sanin yin wani abu ba, kawai idan na yi ana ta magana ina dauka cewa darasi ne hakan a rayuwata."

Rahama ta kuma ce a kullum ita cikin kalubale ta ke ganin yadda ko wace shekara da irin salon da yake zuwa.

Jama'a sun yi martani kan hoton Rahama Sadau ta farin fata

A wani labarin, a wani hoton fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, tare da wani matashi farin fata ya haddasa cece-kuce a kafar sadarwa.

Wani matashi mai suna @essential_ustaz ne ya saka hoton jarumar a shafinsa na Twitter inda ya rubuta cewar jarumar na kara samun ci gaba a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel