Jama'a Sun Yi Cece-Kuce Kan Hoton Rahama Sadau Tare Da Wani Farin Fata

Jama'a Sun Yi Cece-Kuce Kan Hoton Rahama Sadau Tare Da Wani Farin Fata

  • Wani sabon hoton Rahama Sadau ya haddasa cece-kuce a tsakanin mabiya shafukan soshiyal midiya
  • An gano jarumar cikin shiga ta kananan kaya kanta babu dankwali yayin da ta daura hannunta a kafadar wani farin fata
  • Mutane da dama sun yi tir da irin wannan ci gaba da jarumar ta Kannywood ke samu a duniyar masu nishadantar da al'umma

Wani hoton fitacciyar jarumar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, tare da wani matashi farin fata ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Wani matashi mai suna @essential_ustaz ne ya saka hoton jarumar a shafinsa na Twitter inda ya rubuta cewar jarumar na kara samun ci gaba a rayuwarta wanda ga dukkan alamu shagube yake yi mata.

Rahama da wani matashi farin fata
Jama'a Sun Yi Cece-Kuce Kan Hoton Rahama Sadau Tare Da Wani Farin Fata Hoto: @essential_ustaz
Asali: Twitter

Sai dai kuma, saka wannan hoton ke da wuya sai jama'a suka yi caa a kansta inda wasu suka yi tir da irin wannan ci gaba da take samu.

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

A dai hoton, an gano jarumar ne cikin shiga ta kananan kaya kanta babu dankwali sannan hannunta na daure a kan kafadar matashin da ke kusa da ita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a shafin nasa:

"Abun kamar wasa. Rahama fah sai kara samun cigaba take yi kullum!"

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a kan hoton Rahama adau a kasa:

@abdulwaisu ya yi martani:

"Agaskiya @Rahma_sadau anyi Asara ace mutum bayajin Kunyar ALLAH kuma bayajin Kunyar bakin Duniya. Haba Don ALLAH wai kekuwa kina Tunanin Haduwa da ALLAH kuwa?"

@suleimansaeed07 ya ce:

"Da alama cigaba bata yabaka shaawa shege seka bita ai."

@azaabubakar09 ya ce:

"In har wannan shi ne ci gaba Allah ya wadan wannan ci gaban."

@Abuljiddihi ya yi martani:

"Allah ya kyautata muna."

@MUHAMMADGIWAA ya ce:

Kara karanta wannan

“Aiki Ya Yi Kyau”: Matashi Dan Najeriya Ya Kera Motar G-Wagon Da Kayayyakin Gida, Ya Zaga Gari Da Shi a Bidiyo

"Name ginin rijiya amma,lokacinta se taci duniyarta da tsinke kafin adena yayinta kam."

@Ussy_Lima ya ce:

"Dadi sukeji en har anayin topic a kansu. Kamata yayi ayi banza dasu wlh."

@DKawuji ya ce:

"Cigaban zuwa jahanna kenan domin wannan bah har karantarwa bane."

Jarumar Nollywood, Funke Akindele ta magantu a kan mutuwar aurenta 2

A wani labari na daban, jarumar masa'antar Nollywood, Funke Akindele, ta shawarci yan mata da kada su yarda bakin mutane ya kai su ga shiga gidan aure ba tare da sun shirya ba.

Matashiyar ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi kan mutuwar aurenta biyu a wata hira da aka yi da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel