Auren Sayyada Sadiya Haruna Da G-Fresh Al-Ameen Bai Mutu Ba

Auren Sayyada Sadiya Haruna Da G-Fresh Al-Ameen Bai Mutu Ba

  • Labaran mutuwar auren Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen sun cika kafafen sada zumunta musamman TikTok
  • Jita-jitar mutuwar auren na su ta fara ne bayan Sadiya Haruna ta goge dukkanin bidiyoyinta tare da mijin na ta a TikTok
  • Zancen gaskiya shi ne auren taurarin guda biyu yana nan daram babu abinda ya same shi, jita-jita ce kawai ta ƴan kun ji kun gani

Jihar Kano - Jita-jita ta yi ta yawo cewa auren taurarin TikTok, Sayyada Sadiya Haruna da G-Fresh Al-Ameen (Kano state material) ya tunkuyi dusa.

Sai dai, ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya kan batun mutuwar auren na taurarin guda biyu da suka raya Sunnah.

Auren G-Fresh Al-Ameen da Sadiya Haruna bai mutu ba
A watan Yuni dai aka daura auren taurarin biyu Hoto: @gfresh_alameen
Asali: Instagram

An dai ɗaura auren taurarin guda biyu ne a ranar 16 ga Yunin da ya gabata, wanda ya samu halartar manyan jaruman masana'antar Kanmywood.

Kara karanta wannan

Labari Ya Canja: Yan Sanda Sun Binciko Gaskiyar Yadda Wata Budurwa Ta Mutu a 'Hotel'

Yadda jita-jitar mutuwar auren na su ta fara

Jita-jitar mutuwar auren taurarin guda biyu dai ta fara ne bayan da amarya, Sadiya Haruna ta dawo daga aikin Hajji daga ƙasa mai tsarki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An fara ne da yaɗa jita-jitar cewa G-Fresh ya yi yaji daga gidan amaryarsa Sayyada Sadiya Haruna, inda ya koma kwanan shago, bayan sun samu saɓani a tsakaninsu.

Sai dai, binciken da Aminiya ta yi, ya tabbatar da cewa har yanzu auren taurarin biyu yana nan daram bai mutu ba. Kuma igiyar aurensu na nan guda uku ko rawa ba ta yi ba.

Yadda gaskiyar lamarin take

Gaskiyar abinda ya faru shi ne Sayyada Sadiya Haruna ta koma tallata magungunan gargajiya da take sayarwa a shafinta na TikTok..

Hakan ya sanya ta goge dukkanin wani bidiyon taɓara da ta yi a baya, waɗanda suka haɗa har da bidiyoyin kwasar ƙauna tare da su ke yi da mijin na ta.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Magantu Kan Rigimar Da Ta Faru Kan Emefiele a Kotu, Ta Faɗi Matakin Da Za Ta Ɗauka

Wata majiya ta bayyana cewa ganin hakan ne sai ya ƴan tsurkun soshiyal midiya suka fara yaɗa zance cewa aure ya mutu kuma har sun kama gabansu.

Majiyar ta bayyana cewa idan har jita-jitar ba ta lafa ba, ma'auratan na shirin fitar da sanawa akan lamarin.

Fatima Muhammad Ta Yi Martani Ga Wanda Ya yi Mata Kazafi

A wani labarin kuma, jaruma Fati Muhammad ta fito ta fili ta yi martani kan wani da ya yi mata ƙazafi a soshiyal midiya.

Jarumar ta masana'antar Kannywood ta bayyana cewa ba za ta taɓa yafe masa ƙan mummunan ƙazafin da ya jefe ta da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel