"Sai Mun Tsaya Da Kai a Gaban Allah": Fati Muhammad Ta Yi Martani Ga Mutumin Da Ya Yi Mata Kazafi

"Sai Mun Tsaya Da Kai a Gaban Allah": Fati Muhammad Ta Yi Martani Ga Mutumin Da Ya Yi Mata Kazafi

  • Tsohuwar jarumar fim Fati Muhammad ta yi zazzafan martani ga wani da ya yi mata kalamai masu sosa rai a soshiyal midiya
  • Fati ta bayyana cewa ita bata taba zaman banza ba don ko lokacin da ta yi zama a Ingila da aurenta
  • Jarumar ta kuma yi wa mutumin Allah ya isa kan kazafi da batancin da ya yi mata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Fitacciyar tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Muhammad ta mayar da martani ga wani mutum da ya yi mata zafafan kalamai a dandalin soshiyal midiya.

Mutumin dai ya garzaya sashin jarumar na sharhi a soshiyal midiya inda ya yi wasu zafafan kalamai harda alakanta ta da maita, bilicin da sauransu.

Fati Muhammad ta yi wa mutumin da ya yi mata kazafi Allah ya isa
"Sai Mun Tsaya Da Kai a Gaban Allah": Fati Muhammad Ta Yi Martani Ga Mutumin Da Ya Yi Mata Kazafi Hoto: fatymuhd
Asali: Instagram

Ya rubuta a kwamet:

"Tsohuwar mayya, askarawa duk sun gama cinye gindin shegiya kodaddiyaa, duk ta qare yar kutu,mar uba, hoto ba saidai painting a fuska ake yi.

Kara karanta wannan

“A Ina Asibitinka Yake?” Kyakkyawan Likita Ya Tashi Kan Yan Mata Yayin da Ya Saki Zafafan Hotunansa a Wajen Aiki, Sun Zauce

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ban taba zaman Saudiyya ba, Fati Muhammad

Da take mayar masa da martani, jarumar ta bayyana cewa ita ba sauran askarawa bace domin hasalima ita bata taba zama a kasar Saudiyya ba cewa ko a lokacin da ta yi zama a Ingila bisa aiki da aka dauketa da aurenta ta je kuma da aurenta ya mutu ta tarkata ta dawo gida.

Kan cewa da ya yi da ita kodaddiya, Fati ta ce ita bata taba bilicin ba cewa duk wanda ya santa tun da ita fara ce tas. A karshe kuma ta bi shi da Allah ya isa, cewa ba za ta taba yafe masa ba.

Fati ta ce a bidiyon:

"Na ga kwamet dinka ka ce da ni mayya, ka yi munanan kalamai masu zafi a kaina, sauran abubuwan ba sai na fito na fada ba mutane sun riga sun karanta.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Koka Bayan Mai Gidan Da Take Haya Ta Garkame Mata Kofa Kwanaki 4 Da Tarewarta a Gidan, Bidiyon Ya Yadu

"Ka ce dani ni sauran askarawa ce abun da nake son tunatar da kai ni ban taba zaman Saudiyya ba. Tsakanina da Saudiyya sai da na je aikin Hajji ko Umra na dawo.
"Kasar da na zauna ita ce kasar Ingila, kuma da na yi zaman Ingila ban taba zaman kaina ba da aurena na zauna. Lokacin da na tafi Ingila ba zaman kaina na je ba kamfani ne suka dauke ni talla na duniya kuma ban tafi ba sai tare da mijina duk shekarun da na yi a Ingila ban zauna zaman banza ba da aurena kuma da Allah ya kari auren ban zauna a kasar ba na tattara na dawo gida Najeriya, amma ka zo ka yi batanci a gareni ka faffadi abun da ransa yake so.
"Sannan kuma maganar shafe-shafe ko makup bari na baka amsa na farko ni bana bilicin ka tambayi duk wanda ya san ni fara ce tas bana bilicin.

Kara karanta wannan

Saurayi Ya Hana Budurwa Shiga Gidansa Bayan Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Ya Mata Bidiyo

"Magamar kwalliya kuma ai mace yar kwalliya ce ko shekarata 100 ba zai hana ni yin makup ba duk mace yar gyara ce, idan ka fita sauran kasashe za ka ga mace ta tsufa wata ma ta kai shakaru 100 wata bata kai ba amma tana kwalliya. Sabi da haka ni bai dame ni ba.
"Maganar kazafi da ka yi mun da batanci Allah ya isa ba zan taba yafe maka ba, sai mun tsaya a gaban Allah, Allah sai ya saka mun."

Kalli bidiyon a akasa:

Legit.ng ta tuntubi jarumar don jin karin bayani daga bakinta inda ta ce bata dauki mataki a kansa ba amma tana jin yin hakan zuwa nan gaba.

Fati ta ce:

"Lokacin danaga comment din Banji dadi ba ko kadan sbd kazafin yayi muni ga kuma sharri dayamin.
"A yanxu dai babu wani matakin doka ko Shari’a dana dauaka akansa, bansani ba ko nan gaba."

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim Din Kannywood Ya Gamu Da Babbar Jarabawa, Ya Nemi a Taimaka Ma Sa

Jama'a sun yi martani

ummarif_kitchen_utensils ta yi martani:

"Humm wasu dai comments zai ja Masu balai a lahira"

sadia_nas ta ce:

"Wai sai a ce kar a kula irin wadannan, kowa fa yana da zuciya a qirjin shi, ni ta yi ma ni daidai da ta ba shi amsa, kuma barin shi ga Allah shi ne daidai. Ni ma na ce Allah ya bi ma ki hakkin ki."

kano_smart_house ta ce:

"Fati Meye na kula irin wannan mutane irin wannan baa kula su."

mahmud_danmadara ya ce:

"Ni wallahi kece kika bani haushi ma irin wayan nan yaran Basu isa a mayar musu martani Ba yarane kananu kawai sun sami waya Sai suyita zagi da cin mituncin mutane abinda ya kamata dashi kawai kisa a kamashi kuhadu a kotu wanda uwarsa da ubansa sai sun tsugunna sundafa kafafunki dan kutumar ubansa ki daure dan kutumar uba in bai kawo evidence na qazafin da yayi miki ba."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

fatiezee ta ce:

"Yanzu idan aka kama shi sai zama kaman an zuba wa bera ruwan zafi. They think dan suna da waya da data shikenan they can say abinda suka ga dama. Yanzu haka wani dan karamin yaro ne dan cikin mutum."

Momee Gombe ta yi karin haske kan batun soyayyarta da Hamisu Breaker

A wani labarin, jarumar Kannywood wacce tauraruwarta ke haskawa a yanzu, Momee Gombe, ta bayyana cewa babu soyayya tsakaninta da Hamisu Breaker.

Ta bayyana hakan ne a hirarta da Hadiza Gabon cikin shahararren shirin nan na ta 'Gabon's Room Talk Show' da take gabatarwa a YouTube.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng