Rai bakon duniya: Bidiyon yadda aka gudanar da jana'izar daraktan Izzar So, Nura Mutapha Waye, ya yi jama’a

Rai bakon duniya: Bidiyon yadda aka gudanar da jana'izar daraktan Izzar So, Nura Mutapha Waye, ya yi jama’a

  • A karshe an sada babban daraktan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nura Mustapha Waye, da gidansa na gaskiya
  • Mustapha Waye ya yi jama'a sosai a yayin da aka sallaci gawarsa a unguwarsu a jihar Kano a yau Lahadi 3 ga watan Yuli
  • Idan baku manta ba, a yau ne aka tashi da labari mai ban tausayi na rasuwar Nura Mustapha Waye

Dandazon jama’ar Musulmi sun halarci jana’izar babban daraktan masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Nura Mustapha Waye.

A cikin wani bidiyo da jaridar Aminiya ta wallafa a shafinta na Twitter, an gano yadda daruruwan jama’a suka sallaci gawar marigayin.

Yadda aka binne Nura Mustapha Waye
Rai bakon duniya: Bidiyon yadda aka gudanar da jana'izar daraktan Izzar So, Nura Mutapha Waye, ya yi jama’a | Hoto: voanews.com
Asali: UGC

Mustapha Waye ya kasance daraktan fim din ‘Izzar So’ wani shiri mai dogon zango da ake nunawa a dandalin Youtube kuma ya samu karbuwa sosai a tsakanin masoya fina-finan Hausa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa

A safiyar yau Lahadi, 3 ga watan Yuli ne aka wayi gari da labarin rasuwa babban daraktan lamarin da ya jefa masoyansa da abokan sana’arsa cikin dimuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tuni dai abokan sana'arsa suka yi ta wallafa sakonnin addu'o'insu a gare shi.

Ali Nuhu ya rubuta a shafinsa na Instagram:

"Innalillahi wa inna ilaihir raj’un, Allah ya jarabcemu da babban rashin. allah ya jikanta Nura ya kyautata makwanci. Allah ya sa annabi ya karbi bakoncin ka. Jiya war haka muna tare ana ta raha. Allah ya jikanka da rahama."

Sani danja ya rubuta a shafinsa:

"Allah yajikan ka da Rahama Ameen.Allah yabawa yan uwansa hakurin juriya."

Falalu Dorayi ya rubuta:

"INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJI'UN Allah yai maka rahma Nuraddeen.
"Nura Mustapha Waye na daya daga cikin directors da suke taka rawa a Masana’antar Kannywood, Musamman a shirin “IZZAR SO”.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Hoto Da Magana Mai Boyayyen Ma'ana Bayan Jita-Jitar Ganawarsa Da Tinubu a Faransa

"Allah Yai masa gafara ya bawa iyaye da iyalai da Yan uwa hakurin rashinsa. Idan mutuwar tazo Allah kasa mu cika da imani. Amin."

Allah ya yiwa daraktan fim din Izzar So, Nura Mustapha Waye rasuwa

Mun kawo a baya cewa Allah ya yiwa fitaccen daraktan masana'antar Kannywood, Nura Mustapha Waye.

A rahoton da muka samu daga kafar labarai ta DW ya ce, wasu makusanta sun ce an rabu da marigayin da daren jiya cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel