Labaran Kannywood: Lilin Baba Yana Daf Da Auren Ummi Rahab

Labaran Kannywood: Lilin Baba Yana Daf Da Auren Ummi Rahab

  • Akwai alamun cewa mawaki kuma jarumi, mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango, Lilin Baba, ya na gab da angwancewa da jaruma Ummi Rahab
  • A makon da ya gabata jarumar ta nuna wata alama wacce ta janyo rade-radin ya karu bayan ta yi wata wallafa a shafinta na Instagram
  • Ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta, inda ta yi tsokaci da “mijina, masoyina kuma aljannata, hakan ya sa mutane su ka dinga tsokaci

Manuniya tana nuna cewa jarumi kuma mawaki sannan mai daukar nauyin fim din Wuff mai dogon zango ya na gab da auren jarumar da ke haska fim din, Ummi Rahab, Aminiya ta ruwaito.

Akwai labarin soyayyarsu a kwanakin baya wanda hakan ya ja hankalin mutane da dama a ciki da wajen masana’antar.

Kara karanta wannan

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Labaran Kannywood: Lilin Baba Yana Daf Da Auren Ummi Rahab
Lilin Baba Yana Daf Da Auren Ummi Rahab. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

A makon da ya gabata rade-radin ya karu bayan jarumar ta wallafa hoton Lilin Baba a shafinta na Instagram, inda ta kira shi da “Masoyinta kuma mijinta kuma Aljannarta.”

A karkashin rubutun na ta kamar yadda Aminiya ta nuna, mutane sun dinga tsokaci iri-iri har Ali Artwork yana cewa:

“Insha Allah.”

Wani Murtala Bloko ya ce:

“Wanda ba zai iya gani ba ya kau da idonsa.”

Wani Real Adam M Ibrahim ya yi tsokaci inda ya ce:

“Dan bakin ciki sai ya mutu, amma fa ban kama suna ba.”

Ana zargin Adam Zango su ke yi wa habaice-habaicen

Duk da dai ana zargin an yi maganganu da habaicin da Adam Zango ne, amma kuma abin mamakin shi ne har da Murtala Bloko wanda na hannun damar Adam din ne.

Kara karanta wannan

Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi

A kwanakin baya an samu sabani mai yawa tsakanin Adam A. Zango, wanda tsohon Uban gidan Ummi Rahab ne, da jarumar wanda maganganu suka dinga tashi iri-iri.

Ana zargin ya nemi soyayyar jarumar ne amma kuma sai ta ki amincewa wanda hakan ya rura wutar rikicin.

Abin lura anan shi ne yadda yanzu haka jarumar ta ke fitowa a kusan duk wakokin Lilin Baba da fim dinsa.

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel