Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi

Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi

  • Jarumin fim Babanchinedu ya saka baki a sabon rikicin da ya kunno kai a masana'antar tsakanin Naziru sarkin waka da Nafisa Abdullahi
  • Babanchinedu ya ce duk maganganun da Naziru ya yi ba komai bane face haushi da ya ji cewa jarumar ta bar fim dinsa na 'Labarina' mai dogon zango
  • Ya bayyana mawakin a matsayin sarkin mahaukata wanda ya dauki girman kai da izza ya dorawa kansa, baya ganin kowa da mutunci

Babban jarumin Kannywood, Babanchinedu ya shigo cikin fadan abokan sana'arsa Naziru Ahamad wato Sarkin waka da Nafisa Abdullahi.

Babanchinedu ya caccaki Naziru sarkin waka kan kalaman da ya yi game da jaruma Nafisa saboda ta kalubalanci tura yara almajiranci, ya bayyana cewa akwai son zuciya a maganar tasa.

Kara karanta wannan

Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka, ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo

Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi
Sarkin mawaka ko sarkin hauka - Babanchinedu ya yiwa naziru wankin babban bargo kan Nafisa Abdullahi Hoto: 360dopes/bbc.com/Istagram/ babanchinedu
Asali: UGC

Jarumin ya ce ba komai bane ke damun sarkin waka face haushin cewa Nafisa ta bar masu fim dinsu na 'Labarina' saboda zaluncin da aka nuna mata.

A cikin wani bidiyo da ya saki a shafinsa na Instagram, ya bayyana mawakin a matsayin 'sarkin mahaukata' wanda ya dauki girman kai da izza ya daura wa kansa.

"Ina yin shekara hudu baku ji bakina ba, amma idan na fara magana zan iya yi mata shan maganin bature, in yi da safe, in yi da rana, in yi da daddare duka ba matsala bane. Kafin na fara ne dai zai yi wahala.
“Amma ba komai ne nake so in yi magana ba saboda bana son yin magana idan bani da hujja a hannu. Ya kamata ka mallaki hujja kafin ka ce wani abu. Wannan magana da zan yi akan wani abokina da yake ta sakin zance, me ke damun kwakwalwarka.

Kara karanta wannan

Babu wacce iyayenta basu san yadda za su yi da ita ba sama da macen da za ta kama otel tana iskanci - Naziru

“Na san ba daidai kake ba amma ya kamata ka dunga kama kanka, kana kiran kanka sarkin mawaka, ka daura wa kanka sarauta, toh idan dai ka daurawa kanka sarauta dole akwai abubuwan da za ka dunga hakura da su, saboda wannan zai sa ka samu mutuncinka a wuri.
“Jama’a maganar nan da zan yi ba shine nake so yayi alkalanci ba, ku da kuke sauraron mu mutanen kirki ku nake so ku yi alkalanci a kan wannan. Kawai wannan rigimar mahaukacin abokina a kan Nafisa Abdullahi ta ki yi masa fim dinshi ko ta fita a fim din, bai wuce wannan ba.
“Wallahi tallahi ko lamban Nafisa bani da shi, bana waya da ita, tana cikin mutanen da basa cikin layin mutanen da nake hulda da su a masana’antar, amma magana ta gaskiya ne ya zo zan fada wannan gaskiyar ne kawai.
“Nafisa Abdullahi ta saka hannu tana yin aikin fim da kai, ka je bayan fim ya zo karshe ya amsu ya yi kyau, ka je ka amshi kudi ka sayar da fim, ka kawo tallan kamfanin taki, mutum na cikin fim ka bashi N500,000 ko N600,000 ka je kai kuma ka amshi miliyan 100 ko 150 kawai yana cikin fim sai a kawo mashi tallan wani abu a cikin fim ba wai a tashan ba. Ko kuma a cikin fim din a sa su dunga tallan abu na gwamnati.

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

“Tallan gwamnati ba wani abu bane ko tallan koma menene z aka iya yi a cikin fim dinka bai karya ka’ida na fim ba amma jaruman da ke aikin a cikin fim din ya kamata a sanar da su cewa fim dinnan yanzu ya karkata ne wajen tallan gwamnati. Kowa ya sani kai ba masoyin gwamnati bane, baka yin gwamnati, ba mai kaunar gwamnati bane amma saboda kudin da ka sha miliyoyin daruruwa ka zo kana tallan gwamnati a ciki.
“Mutanen da kuke kallon fim din ku je ku duba idan baku duba ba, ku je ku ga a cikin fim dinnan nasu ana tallan gwamnati ko ba’a yi, karya nake yi ko gaskiya ne. kuma ku duba dukka abubuwan shi akwai inda yake harkar gwamnati, shi baya harkar gwamnati amma ya amshi miliyan daruruwa na gwamnati yana tallan noma da sauran abubuwa da gwamati ke yi, su kuma yana basu N500,000 ko 300.

Kara karanta wannan

Daga Landan zuwa Lagas: 'Yan Najeriya 3 da suka yi tafiyar ban mamaki a kafa da babur

“Wannan bai zama adalci ba don haka yara sun nuna maka toh wannan fa ba daidai bane ta yaya za a yi mana haka ka nuna basu isa ba saboda dama kai ko makwabtanka baka zaman lafiya da su, kowa kana kallonsa bai isa ba. Ka raina kowa saboda kana ganin kanka basarake.
“Sarkin mawaka wani sarauta ne? akwai sarkin yan daudu ma, akwai sarkin karuwai, kowa akwai sarkinsa, sarkin tasha ba wanda babu amma ka dauki kanka kana ganin kanka kai sarkin duk duniya ne kowa ka ma fi karfinsa kana girman kai.
“Toh ka fito a fim dinka mana tunda kaima ka fara wasa kana son a taimakeka ka zama jarumi a cikin fim, kai jarumi ne a waka amma ba jarumi bane a fim, idan ta kaine mutane ma baza su kalli fim din ba ma saboda a cikin fim dinma kana nuna masu isa a cikin fim din. Waye kai kana nuna masu takama, zaka nunawa yan kallo takama ne? duk abun da ake yi muna dai rufa maka asiri ne amma yarinya ta zo ta fita a fim saboda gwamnati sun daina baka kudi a fim din kana ganin ta cuce ka, itace fim din, da kun cire ta a fim ya mutu, wa zai bi kuma ya kalla. Ita ake kallo da wannan yaron, su biyu. Kun cuce su sun ce basa yi kuma na menene za ka zo kana mata hauka.

Kara karanta wannan

A karon farko, Jaruma Hadiza Gabon tayi martani ga masu cewa tana kyautar Riya

“Ta yi magana, maganar da ta yi ka zo ka karkata magana, ka juya magana amma duk wanda ya kalli maganarta kuma ya saurari naka zai gane akwai wani abu ne a cikin ranka na daban, duk mai hankali so kake ka juya mata magana. Kai idan ana maganar almajirai wanene kai da z aka yi magana, ka manta wanda ya watsowa wannan tsohuwar almajiran ruwan zafi a kofar gidansa.”

Baki da ilimin addini - Fati Slow ta shigarwa sarkin waka, ta yiwa Nafisa Abdullahi wankin babban bargo

A baya mun ji cewa tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da aka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arsu, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ‘ya’yansu almajiranci.

Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

Tsohuwar jarumarta bayyana cewa sai inda karfinsu wajen fada ma duk mutumin da zai zagi almajirai gaskiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel