Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo

  • Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana kaduwa da firgici da jin labarin mutuwar mutane a jihar Imo
  • An ruwaito a baya yadda wata haramtacciyar matatar mai ta fashe a jihar Imo, mutane sun halaka
  • Shugaban ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da cewa, kada su bari hakan ya sake faruwa a ko ina a Najeriya

Abuja - Shugaba Buhari ya fusata, ya ba jami'an tsaro umarnin kara kaimi wajen kawo karshen haramtattun ayyuka daga haramtattun matatan man fetur da ke aiki ba bisa ka'ida ba a yankunan kasar nan.

Hakazalika, shugaban ya bayyana kaduwarsa da jin labarin mutuwar mutane sama da 100 sakamakon irin wannan lamari a jihar Imo.

Fusatar Buhari na zuwa ne bayan wani rahoton mutuwar sama da mutane 100 ne a daren Juma’a bayan da wata matatar man fetur ta fashe a dajin Abaezi da ke karamar hukumar Ohaji-Egbema a jihar Imo ta Kudu maso Gabashin Najeriya ya karade kafafen yada labarai.

Kara karanta wannan

Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo

Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin mutuwar 'yan Imo
Kada haka ta sake faruwa: Shugaba Buhari ya kadu da jin labarin salwantar rayuka 100 a Imo | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Al’ummar da alamarin ya shafa tana kan iyaka ne tsakanin jihohin Ribas da Imo, inji rahoton SaharaReporters.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika motoci da dama sun kone yayin iftila'in, lamarin da ya jefa al’ummar cikin fargaba.

PM News ta ruwaito cewa, ta samo batun na Buhari ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ya kuma bayyana lamarin a matsayin “musiba da bala’in kasa.”

Buhari ya ce dole ne a daura alhakin asarar rayukan bayin Allah da dukiyoyinsu kan masu haramtacciyar matatar man "wadanda dole ne a kama su kuma a hukunta su."

Shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa da kuma nuna matukar kaduwa da firgici da jin lamarin kana ya mika jaje ga iyalan wadanda abin ya rutsa dasu, al’ummar Ohaji Egbema da gwamnati da jama’ar jihar Imo.

Kara karanta wannan

Ku yi koyi da Dangote: Buhari ya ba 'yan kasuwan Najeriya shawari mai ban mamaki

Ya kuma umarci ’yan sanda, da jami'an sirri da kada su sake barin faruwar lamari irin wannan mai ratsa zuciya a wani yanki na kasar nan.

Ba wannan ne karon farko da ake samun irin wannan hadari a yankunan Kudu ba, kasancewar ana yawan samun haramtattun matatun man fetur.

Sama da rayuka 100 sun salwanta sakamakon gobara da ta tashi a matatar man fetur din sata a Imo

A tun farko, a kalla rayuka 100 ne suka salwanta sakamakon fashewar wani abu a matatar man fetur na sata dake Ohaji a karamar hukumar Egbema ta jihar Imo.

Lamarin, wanda ya fara wurin karfe 11 na daren Juma'a, ya yi sanadiyyar tashin gagarumar gobara a Ohaji da ke yankin Egbema, Thecable ta ruwaito.

A yayin jawabi kan lamarin, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ya samu wakilcin Goodluck Opiah, kwamishinan lamurran man fetur, ya ce matasa da yawa sun rasa rayukansu sakamakon gobarar, amma har yanzu ba a kididdige yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

Asali: Legit.ng

Online view pixel