Kannywood: Matar jarumi Adam A Zango ta haihu, an samu diya mace

Kannywood: Matar jarumi Adam A Zango ta haihu, an samu diya mace

  • Shahararren jarumin Kannywood, Adam A Zango ya samu karuwa tare da amaryarsa Safiya Umar Chalawa
  • Allah ya azurta jarumin da iyalinsa da samun haihuwar diya mace
  • Abokiyar sana'arsa, jaruma Maryam KK ce ta sanar da labarin haihuwar a shafinta na soshiyal midiya

Kaduna - A yau Alhamis, 4 ga watan Nuwamba ne muka samu labarin cewa amaryar shahararren jarumin nan na Kannywood, Adam A Zango watau Safiya Umar Chalawaa ta samu karuwa.

Legit Hausa ta samu labarin haihuwar ne a shafin abokiyar sana'arsa Maryam KK na Instagram, inda ta taya ma'auratan murnar wannan kyauta da Allah ya yi masu.

Kannywood: Matar jarumi Adam A Zango ta haihu, an samu diya mace
Kannywood: Matar jarumi Adam A Zango ta haihu, an samu diya mace Hoto: @adamazangoofficial_.
Asali: Instagram

A cewar Maryam KK, Allah ya azurta ma'auratan ne da samun santaleliyar diya mace.

Kara karanta wannan

Dama can ni Musulma ce kuma 'yar Saudiyya, kawai Sallah ne bana yi - BBNaija Gifty

Ta rubuta a shafin nata:

"Barka Yarima Allah ya raya mana "

Tuni dai mabiya shafin nata suka shika sashin sharhi domin yi wa jarumin da iyalinsa addu'a da fatan alkhairi bisa ga wannan babban kyauta da suka samu.

Legit.ng ta zakulo wasu daga cikin sharhin:

chaibou8158 ya yi martani:

"masha allah.allah yarayata"

honibrahimdikko ya rubuta:

"Masha Allah❤️❤️❤️"

abkhan_muhd ya ce:

"Allah ya rayata bisa sunnah"

official_kannywood_fan_page ta rubuta:

"Alhamdulillah Allah ya raya @adamazangoofficial_ @maryamkk___"

mr_musa_zaheer ya ce:

"@maryamkk___ Allah raya amma nayi kamu❤️❤️❤️"

'Yar Aljannah: Kofa a bude take ga kishiya - Martanin amaryar Adam A Zango ga wata budurwa da ta bayyana tana son mijinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa amaryar fitaccen jarumi Adam A Zango ta wallafa wani hoto na mijin nata inda ta rubuta cikin harshen turanci cewa; "Mijina abin alfahari na ina sonka so mai tsanani," amaryar ta yi rubutun ne cikin takaitattun harufa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan arewa sun nuna goyon bayansu ga shahararren dan siyasar kudu

Koda ta wallafa wannan hoto da wannan rubutu sai aka samu wata me karfin hali a cikin 'yan matan dake bibiyar shafinta tayi tsokaci da harshen na turanci itama cewa nima ina son shi dan Allah ki amince in zamar miki abokiyar zama.

Safiyya amaryar Adam Zango ba ta yi kasa a guiwa ba ta mayar da amsa da cewa kofa a bude take.

Sai dai bayan nan kuma Safiyya ta kwafo wannan magana ta waccan yarinya ta sake wallafawa a shafinta kana ta kara tabbatar mata da cewa kofa fa a bude take.

Asali: Legit.ng

Online view pixel