Dama can ni Musulma ce kuma 'yar Saudiyya, kawai Sallah ne bana yi - BBNaija Gifty

Dama can ni Musulma ce kuma 'yar Saudiyya, kawai Sallah ne bana yi - BBNaija Gifty

  • BBNaija Gifty Powers ta baiwa mabiyanta mamaki kan shafin Instagram lokacin da ta sanya Hijabi
  • 'Yar wasan ta bayyanawa mabiyan cewa tuni dama ita Musulma ce kawai dai ba ta Sallah ne da ibadah
  • Gifty ta ce ta sanya Hijabi saboda ita yar kasar Saudiyya ce asalinta amma ba'a tilasta mata sanyawa ba

An ga BBNaija Gifty Powers sanye da Hijabi karo na farko a hotunan da ta daura a shafinta na Instagram.

Kuma duk a lokaci guda, 'yar wasar ta sanye tsarkan salibi.

A maganar da tayi kan hotunan, Gifty tayi rubutun addu'a da larabci wanda muka fassara matsayin godiyanta ga Allah bisa ni'imomin da yayi mata.

Tace:

"A al'ada fa ni Musulma ce, ni Musulma ce tun haihuwa na, amma bana Sallah."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun kai hari Jami'ar Abuja SQ, sun kwashe ma'aikata da 'yayansu

"Mata na sanya Hijabi ne don rufe jikinsu saboda kada wasu mazaje da ba muharramansu suga jikinsu."

BBNaija Gifty
Dama can ni Musulma ce kuma 'yar Saudiyya, kawai Sallah ne bana yi - BBNaija Gifty Hoto: officialgiftypowers
Asali: Instagram

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu

Bala Ahmad:

Mai makon kuyi mata addu'a Allah ya shiryeta kunata zaginta... why ,kai kanada tabbacin lahira ne? Sai ta wuce ta barku

Abdul Jalil:

Fatan shiriya. Allah ya gafarta mana gaba ki daya.

Safa'atu Abdullahi Abdullahi:

Cab aikina ruwa wallah sallah ita ta banbance tsakanin musulmi da kafiri ashekowa tunda bakya sallah sunanki kafura gidi

Saifullah Adamu Muhammed:

Amma wannan ta rainawa mabiyantan hankali. Yanzu yakamata kifada musu kindawo sallan ne kokuma haryanzu ajjihun bayane ke?

Kz Alkali:

Ki daina alakanta kanki da musulunci don bayan Imani da Allah da manzon sa babu Abu mafi mahimmanci a musulunci Sai sallah

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

Munnirah Abdussalam Gusau:

Subhanallah
Allah yasa kina da rabon yin tuba

Asali: Legit.ng

Online view pixel