'Yar Aljannah: Kofa a bude take ga kishiya - Martanin amaryar Adam A Zango ga wata budurwa da ta bayyana tana son mijinta

'Yar Aljannah: Kofa a bude take ga kishiya - Martanin amaryar Adam A Zango ga wata budurwa da ta bayyana tana son mijinta

- Amaryar da jarumi Adam A Zango ya auro watannin da suka gabata ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram da ya jawo hankalin mutane da yawa

- Amaryar ta wallafa irin soyayyar da take yiwa mijin nata, sai dai kuma wata yarinya ta nuna cewa ita ma tana son mijin nata idan za ta yadda ta zama abokiyar zamanta

- Amaryar ba ta yi kasa a guiwa ba ta bayyana cewa kofa a bude take idan har tana so ita ba ta da damuwa

A 'yan kwanakin nan amaryar fitaccen jarumi Adam A Zango ta wallafa wani hoto na mijin nata inda ta rubuta cikin harshen turanci cewa; "Mijina abin alfahari na ina sonka so mai tsanani," amaryar ta yi rubutun ne cikin takaitattun harufa.

Koda ta wallafa wannan hoto da wannan rubutu sai aka samu wata me karfin hali a cikin 'yan matan dake bibiyar shafinta tayi tsokaci da harshen na turanci itama cewa nima ina son shi dan Allah ki amince in zamar miki abokiyar zama.

Safiyya amaryar Adam Zango ba ta yi kasa a guiwa ba ta mayar da amsa da cewa kofa a bude take.

KU KARANTA: Tirkashi: Tallar rigar nono ya jawowa jaruma Maryam Booth bakin jini ga masoyanta

Sai dai bayan nan kuma Safiyya ta kwafo wannan magana ta waccan yarinya ta sake wallafawa a shafinta kana ta kara tabbatar mata da cewa kofa fa a bude take.

Wannan sake wallafa jawabin da tayi sai yasa wasu ke mata martani da cewa maganar ta dame ta ne shi yasa har ta sake kwafo zancen yarinyar ta wallafa saboda kishi na damunta shi yasa ta kasa mantawa.

Ga dukkan alamu wannan martani bai yiwa amaryar dadi ba dan haka tayi wani dogon rubutu ta wallafa a shafin nata wanda har ya bawa angon nata dariya shima ya sake wallafawa a shafinsa, sannan ya rubuta a kasa cewa kin sani dariya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel