Ku rage yawan haihuwa domin 'ya'yanku su samu ilimi - Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi kira ga al'umma su rage haihuwa barkatai kayyade yawan al'umma nahiyar Afrika inda yace adadin yaran da basu zuwa makaranta a Kano sun kai miliyan uku.
Ganduje ya fadi hakan ne jawabin da ya yi ranar Alhamis a Cibiyar harkokin kasa-da-kasa wato Chatham House dake Ingila inda yace adadin al'ummar Afirka na karuwa sai dai ba'a tanadin yadda za'a ilimantar dasu.
"Abu guda dake banbanta yawan al'umma tsakanin kasashen duniya shine ilimi, idan akwai tarin al'umma kuma suna da ilimi, yawansu zai kawo musu cigaba amma idan babu ilimi, zai janyo matsala," inji Ganduje.
DUBA WANNAN: Shugabanin kungiyar masoya Buhari sun kai ziyara fadar gwamnati, kalli hotuna
"Idan muka duba kasashe 10 da su kafi ilimi a Afirka; Seychelles, Equatorial Guinea, Afirka ta Kudu, Sao Tome, Libya, Namibia, Mauritus, Cape Verde, Botswana, Swaziland da Zimbabwe - zamu gane cewa duk kasashe ne masu al'umma kadan," inji Ganduje.
Gwaman wanda ya yi digirinsa a jami'ar Ibadan, ya bayar da shawarwari game da maudu'in taron mai taken 'Higher Education and Demographic Growth in Africa' yace nahiyar Afirka na bukatar fara tsare-tsare na bunkasa gine-gine saboda gaba tare da kuma kayyade yawan al'umma.
"Muna da dalibai fiye da miliyan uku a Kano, adadin yaran da basu zuwa makaranta suma sun haura miliyan uku. Saboda haka idan muna magana a kan Afirka, shin zamu iya cewa yawan mutanen mu ya yi dai-dai da irin Ilimin da muke bayarwa. Hakan kuwa zai haifar mana da Alkahiri?
"Ana cewa kasar Ingila ta kayyade yawan al'umman ta na tsawon shekaru amma Najeriya da Afirka sai karuwa mu keyi. Amma a zahiri wani irin karuwa ce tunda bamu da tattalin arzikin da zamu kula da kanmu.
Tunda bamu da karfin tattalin arziki, dole zamu mayar da hankali wajen kawo cigaba da gine-gine amma ya zama dole mu dauki mataki kan yadda muke hayayafa. Ta hakan ne za'a ci nasara.
A kididigar da UNESCO tayi a Najeriya, fiye da 10.5 miliyan suna zauna kara zube basu zuwa makaranta. Babu wata kasa a duniya dake da irin wannan yawan yara marasa zuwa makaranta kamar yadda The Cable ta wallafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng