Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje

Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje

- A ci gaba da Najeriya ke samu a fannin kimiyya da fasaha, an kirkiri jirgi mai saukar ungulu

- Kasar ta fitar da jirgi mai saukar ungulu da wasu abubuwa masu ban mamaki zuwa kasashen ketare

- Ci gaban ya yi sanadiyyar samun kudaden shiga ta kasashen ketare da haura tiriliyoyin naira

Najeriya ta yi fiye da fitar da danyen mai kadai da wasu kayayyakin amfanin gona a shekarar 2020, ba tare da wani abin a zo a gani ba a bangaren fasahar zamani, Premium Times ta ruwaito.

A matsayinta na kasa mai dogaro da shigo da kayayyaki, kasar ta yi shekara da shekaru tana kokarin samar da kudaden shiga ta kasashen waje da kuma habaka darajar Naira, kasar na kuma fama da gibin cinikayya da ake samu.

Yayin da take shigo da komai daga kayan fasahar zamani zuwa waken soya zuwa abun tsokale hakori, babban abin da Najeriya ke fitarwa shine danyen mai. Hakanan ana sayar da koko, Kashu da wasu kayan amfanin gona.

Amma a cikin kwata na hudu na 2020, yayin da cutar ta Korona ta yi fata-fata da tattalin arziki, Najeriya ta fitar da wasu kayayyakin ƙere-ƙere da fasaha.

KU KARANTA: Ba zan bari 'yan ta'adda su lalata mana tsarin ilimi ba, in ji shugaba Buhari

Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje
Jirgi mai saukar ungulu da sauran abubuwa 4 masu ban mamaki da Nigeria ta kera ta siyar a waje Hoto: Pratt & Whitney
Asali: UGC

Rahoton cinikayya na baya-bayan nan na Hukumar Kididdiga ta Kasa da aka fitar a makon da ya gabata, ya lissafa na farko da cewa, an fitar da jirage masu saukar ungulu.

Biyo bayan jiragen, kasar ta fiitar da dandamalin hako na jirgin ruwa ko ruwa, ababen kira na jiragen ruwa, wasu injuna masu tuka kansu da kuma kayan shawagi.

Darajar cinikin kayayyakin da aka ƙera a kwata na hudu na 2020 ya tsaya a kan naira tiriliyan 3,955, wanda ke wakiltar 43.4% na jumillar cinikin. Daga wannan, bangaren fitar da kaya ya kai naira biliyan 129.

Kasar ta fitar da jirage masu saukar ungulu marasa nauyi wanda basu wuce kilogiram 2000 zuwa kasar Ghana, wanda darajarsu ta kai naira biliyan 10.5 duk da cewa babu tabbas ko an yi amfani da jirage masu saukar ungulun.

Fitar da kayan masarufi, wanda a karkashinsa ne aka rarraba jiragen masu saukar ungulu, yakai naira biliyan 129 a cikin kwata.

Sauran kayayyakin da kasar ta fitar da su sun kasance dandamalin hako mai ne na ruwa, wanda aka fitar dashi zuwa kasashen Kamaru da Equatorial Guinea. Suna da daraja naira biliyan 76.73 da biliyan 10.2 bi da bi.

An fitar da ababen kiran jiragen ruwa da kudinsu ya kai naira biliyan 7.2 zuwa kasar Indonesia, sannan an sayar da wasu injunan ga kasar Ivory Coast, wanda ya kai naira biliyan 6.4.

Tsakanin watannin Oktoba zuwa Disamba 2020, Najeriya ta kuma fitar da kayan aikin gona da darajarsu ta kai naira biliyan 56.

Kasar ta kuma fitar da kayan masarufi da suka kai naira biliyan 47, daskararrun ma’adanai kan naira biliyan 4, kayan makamashi a kan naira biliyan 5, da danyen mai da sauran albarkatun man fetur a kan naira tiriliyan 2.9.

KU KARANTA: An kashe matar tsohon kwamishinan ‘yan sanda a jihar Benue

A wani labarin, Shugaban jami’ar Adeleke, Farfesa Solomon Adebiola, ya bayyana cewa riga-kafin kwayar cutar COVID-19 da masana kimiyya na Najeriya suka kirkiro a halin yanzu tana matakin gwaji na asibiti, Vanguard News ta ruwaito.

Ya kara da cewa allurar, wacce Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita kuma ta sami goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samu ne daga wani masanin kimiyya daga Jami’ar Adeleke, Dokta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar wasu daga wasu jami’o’i biyar na kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel