Sunaye da Bayanan Kasashen Afrika 8 da Sojoji Suka Yi Juyin Mulki a Shekaru 5

Sunaye da Bayanan Kasashen Afrika 8 da Sojoji Suka Yi Juyin Mulki a Shekaru 5

Benin - Wani yunkuri na juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi ya sake jefa nahiyar Afrika cikin fargaba, yayin da sojoji suka bayyana cewa sun kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Duk da sanarwar juyin mulki da sojojin suka yi, fadar kasar Benin ta tabbatar da cewa Talon yana cikin koshin lafiya, kuma rundunar sojin kasa, mai biyayya ga dimokuradiyya ta fara dawo da ikon ta.

Kasashe 8 na Afrika sun fuskanci juyin mulki a cikin shekaru 5
Sojoji sun yi juyin mulki a Burkina Faso, Nijar da wasu kasashen Afrika. Hoto: @GoitaAssimi
Source: Twitter

Wannan yunkurin ya kara shiga jerin juyin mulki da dama da suka yiwa Afrika katutu cikin shekaru biyar, inda dukkansu ke nuna karuwar raguwar tasirin siyasar farar hula da karuwar ikon sojoji a wasu yankuna, in ji rahoton Punch.

Kasashen Afrika da sojoji suka yi juyin mulki

Legit Hausa ta zakulo kasashen da sojoji suka yi wa juyin mulki a Afrika daga 2020 zuwa 2025:

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi halin da ake ciki bayan yunkurin juyin mulki a Benin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Mali — Agusta, 2020

A watan Agusta, 2020, hafsoshin soji guda biyar suka hambarar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keita, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna. Tsakanin Mayu 2021, soji suka sake karbe mulki daga gwamnatin rikon kwarya.

Kanal Assimi Goita ya zama shugaban rikon kwarya, inda daga baya ya soke zaben da aka tsara na Fabrairun 2024, yana mai zargin cewa akwai matsalar tsaro.

A watan Yuli, 2025, Goita ya sa hannu kan dokar da ta bashi wa’adin shekara biyar a mulki, ba tare da zabe ba. Su kuwa kungiyoyin jihadi, suka ci gaba da raunata mulkin Goita da takunkumi kan mai.

2. Guinea — Satumba, 2021

A ranar 5 ga Satumba, 2021, hafsoshin soji karkashin Laftanal Kanal Mamady Doumbouya suka kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Condé.

Doumbouya ya jagoranci gwamnatin soja, kuma a watan Nuwamba 2025 ya mika takardun takarar shugaban kasa domin zaben ranar 28 ga Disamba, wanda ake fatan ya dawo da tsarin dimokuradiyya a kasar.

Kara karanta wannan

Ya matso kusa da Najeriya: Sojoji sun sake juyin mulki a Afrika ta Yamma

3. Sudan — Oktoba, 2021

A Sudan, bayan rikice-rikicen siyasa tsakanin sojoji da farar hula, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya karbe mulki a ranar 25 Oktoba 2021.

Daga shekarar 2023, kasar ta fada yakin basasa tsakanin sojojin kasa da dakarun RSF, karkashin Muhammad Hamdan Daglo.

Wannan yaki ya jawo mutuwar dubban mutane, ya kuma jefa kasar cikin mummunan bala’in jin kai, in ji rahoton BBC.

4. Burkina Faso — Janairu da Satumba 2022

A 2022, an sami juyin mulki biyu a Burkina Faso. Na farko ya kifar da Shugaba Roch Marc Christian Kaboré, karkashin Lt-Kanal Paul-Henri Damiba.

A Satumba 2022, wasu ragowar sojoji suka kifar da Damiba, inda Kyaftin Ibrahim Traoré ya hau mulki. A 2024, an kayyade masa karin shekaru biyar a mulki saboda yawaitar hare-haren jihadi.

5. Nijar — Yuli, 2023

A Yuli 2023, sojojin gadin shugaban kasa suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum wanda aka zaba a 2021. Janar Abdourahamane Tiani ya karbi madafun iko.

Kara karanta wannan

Buhari, Natasha da wasu fitattun ƴan Najeriya da aka fi karanta labaransu a 2025

A 2025, gwamnatin rikon kwarya ta kara wa’adin shekaru biyar ga Tiani sakamakon tabarbarewar tsaro da ayyukan kungiyoyin jihadi.

6. Gabon — Agusta, 2023

An hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba a ranar 30 Agusta 2023, bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe mai cike da cece-kuce.

Janar Brice Oligui Nguema ya karbi mulki, daga bisani ya lashe zaben dimouradiyya da aka gudanar a Afrilu 2025 da kaso 94.85 cikin 100, in ji wani rahoto da aka wallafa a WikiPedia.

Sojoji sun kwace mulki daga Shugaba Andry Rajoelina a cikin watan Oktoba, 2025.
A ranar 17 ga Oktoba, 2025 ne aka rantsar da Kanal Michael Randrianirina matsayin shugaban kasar Madagascar na wucin gadi. Hoto: Anadolu / Contributor
Source: Getty Images

7. Madagascar — Oktoba, 2025

A Madagascar, makonni na boren matasa na “Gen Z” ya kai ga sojoji sun kifar da Shugaba Andry Rajoelina, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Kanal Michael Randrianirina ya zama shugaban kasa tare da alƙawarin gudanar da zabe cikin shekara guda zuwa shekara biyu.

8. Guinea-Bissau — Nuwamba, 2025

Legit Hausa ta rahoto cewa sojoji a Guinea-Bissau sun ayyana cewa suna da cikakken iko a kasar, tare da rufe iyakoki da dakatar da tsarin zabe.

Kara karanta wannan

Majalisa ta kira Janar Musa da ministoci 2, za a binciki yadda suka kashe $30m

Rundunar hadin gwiwa daga bangarorin sojoji kala-kala ce ta karbi ragamar mulki, lamarin da har ya sa ECOWAS ta dakatar da kasar daga cikin kungiyar.

Juyin mulki: Halin da ake ciki a Benin

Tun da fari, mun ruwaito cewa, wasu sojoji da suka kira kansu “kwamitin sojoji na sake gina kasa” (CMR) sun sanar da cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon.

Sai dai, bayan wasu 'yan awanni da sanarwar, masu tsaron lafiyar shugaban kasar sun ce yana cikin koshin lafiya, kuma rundunar sojojin kasar na sake samun cikakken iko.

Wani jami’in soja ya tabbatar da cewa ana kula da lamarin, kuma masu yunkurin juyin mulkin ba su karbe fadar shugaban kasa ko ofishin Patrice Talon ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com