Bincike: Sojojin da suka hambarar da mulki a Guinea sun samu horon Amurka
Tare da jin karar harbe-harbe da suka mamaye zagayen fadar shugaban kasar Guinea a Conakry, wata babbar runduna ta musamman karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumdouya mai shekaru 41 ta hambarar da Shugaba Alpha Conde daga kan karagarsa, wanda ya kawo karshen mulkin dimokuradiyyar kasar a ranar Lahadi, 5 ga watan Satumba.
Bincike ya nuna cewa, Kanal Doumbouya da tawagarsa ta juyin mulkin ba baki bane ga sojojin kasar Amurka (US).
Majiyoyi masu tushe kamar na New York Times da Daily Mail sun bayyana cewa matashin sojan da ya ayyana kansa a matsayin sabon jagoran Guinea a lokacin yana jagorantar wata runduna ta sojojin da Green Berest na Amurka ke horarwa tun daga watan Yuli.
Wannan shine dalilin da yasa masu horarwar, suka ji kunyar abin da wadanda suka horar suka yi, suka tuka motarsu zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke babban birnin kuma nan da nan suka dakatar da shirin horarwar a yayin da ake shirin juyin mulkin.
Amurka ta nisanta kanta da juyin mulkin Guinea
Da take nisanta kanta daga abin da ya faru, Rundunar Amurka a Afirka, ta bakin mai magana da yawun ta, Kelly Cahalan, ta bayyana karara cewa juyin mulkin ba ya cikin shirin horon kuma bai yi daidai da "horon soja da koyarwar Amurka" ba.
Da yake kan irin wannar matsaya, wani jami'in hulda da jama'a na rundunar, Bardha S. Azari, ya ce:
"Ba mu da wani bayani game da kwace mulki da sojoji suka yi kuma ba mu da masaniyar faruwar hakan."
Doumbouya wanda ya yi aiki da rundunar sojan Faransa na dogon lokaci kuma da ke cikin atisayen sojan Amurka ya tsere don kitsa juyin mulkin a cikin sa’o’in sanyin safiya.
Wannan dalili ya kara rura wutar shakku kan cewa watakila jami'an na Amurka suna bacci ne lokacin da ya zille daga cibiyar da ke Forécariah tare da abokan aikinsa.
Tashin hankali yayin da sojojin Guinea suka kame shugaban kasa, suka kwace mulki
A wani labarin, Rahoton BBC ya nuna cewa ba a san makomar shugaban kasar Guinea, Alpha Condé ba bayan wani faifan bidiyo da ba a tantance ba ya nuna shugaban a hannun sojoji, wadanda suka ce sun yi juyin mulki a kasar.
Legit.ng ta tattaro cewa, ministan tsaron kasar, duk da haka, an ambato shi yana cewa yunkurin juyin mulkin ya ci tura.
A cewar rahoton, wannan ya biyo bayan harb -harben da aka shafe sa'o'i ana yi a kusa da fadar shugaban kasa a Conakry babban birnin kasar yayin da sojoji ke sintiri kan titunan da ba kowa a kai.
Asali: Legit.ng