Japa: Ƙasashe 3 da Ke ba Ƴan Najeriya Biza da Takardar Zama Ɗan Ƙasa cikin Sauƙi
A da, yawancin ’yan Najeriya suna kallon Amurka, Birtaniya da Kanada a matsayin manyan kasashen yin 'japa', watau ƙasashen da za su je neman kuɗi.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amma saboda yawan ƙin amincewa da takardar biza da kuma tsadar rayuwa, mutane da yawa sun fara waiwayen wasu ƙasashe da ke ba da biza cikin sauƙi.

Source: Getty Images
Kasashe 3 masu ba da biza cikin sauƙi
Abin sha'awa, akwai ƙasashen da ke ba baƙi biza cikin sauƙaƙe, sannan suna da sauƙin rayuwa, da sauƙin samun takardar zama dan ƙasa, inji rahoton Vanguard.
Idan ka shirya fita waje domin neman kudi, to ga wasu ƙasashe uku masu da ya kamata ka duba tsarinsu, ko zai dace da buƙatarka:
1. Germany
Jamus ta zama ɗaya daga cikin manyan kasashe da 'yan Najeriya ke zuwa don neman damarmakin neman kudi.
Akwai bizar masu neman aiki da ake kira 'Job Seeker Visa,' wacce ke ba ƙwararrun mutane damar zuwa Jamus su zauna tsawon watanni shida suna neman aiki.
Ga ɗalibai, kuɗin karatu ba shi da tsada idan aka kwatanta da ƙasashen Yamma, sannan bayan kammala karatu, akwai damar samun bizar 'post-study work' don yin aiki a kasar.
Buƙatar ƙwararrun ma'aikata a fannoni kamar IT, aikin injiniya, da kiwon lafiya ya sa Jamus ta zama babbar kasa ga waɗanda ke son zuwa waje cirani.
2. Australia
Asturaliya tana amfani da tsarin ƙaura da ke ba da dama ga matasa masu ƙwarewa a fannoni da dama, a cewar rahoton shafin GMS.
Gwamnati na bukatar kwararrun matasa a fannonin kiwon lafiya, malamai, IT, da gine-gine, wanda ke ba wa 'yan Najeriya da ke da ƙwarewa damar samun takardar zama a kasar.
Bizar wucin-gadin Asturaliya tana sauƙaƙa wa ɗalibai shiga sahun masu neman aiki, ko kuma masu yin aiki bayan sun kammala karatu.
3. Portugal
Portugal ta zama ɗaya daga cikin kasashen da mutum zai zauna a cikinta, saboda saukin samun bizarta da guraben ayyukan da take da su.

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
'Yan Najeriya za su iya zama a kasar ta hanyar bizar "D7 Visa" (ga masu samun kuɗi mai yawa ko masu aiki daga gida) da kuma "Golden Visa" (ga masu zuba jari).
Farashin rayuwa a Portugal ya fi rahusa idan aka kwatanta da yawancin ƙasashen Turai. Bayan shekaru biyar kacal na zama, mutum na iya neman zama ɗan ƙasa.
Wannan babbar damar ta sanya Portugal ta zama babbar kasa ga masu shirin zuwa waje cirani, da kuma masu burin zama a kasashen Turai.

Source: Getty Images
Babu aiki: Matashi ya dawo gida daga Kanada
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani matashi dan Najeriya ya dawo gida, bayan shafe dogon lokaci yana neman aiki a kasar Kanada, ba tare da ya samu ba.
Matashin, ya ce ya bar Najeriya zuwa Kanada da zummar samun rayuwa mai kyau, amma sai ya tsinci kansa a cikin damuwa mai yawa, saboda rashin aikin yi.
Ya ce bayan zaman dirshan da ya yi yana tunani, a karshe dai ya fahimci cewa duk tsananin rayuwa a Najeriya, gwanda ya dawo gida da ya ci gaba da zama a Kanada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
