Kasashen Turai sun fi tausayi da taimakon jihar Borno a kan kasashen Larabawa

Kasashen Turai sun fi tausayi da taimakon jihar Borno a kan kasashen Larabawa

- Gwamnan Babagana Umara Zulum, ya ce kasashen Turawa sun fi nuna damuwa da halin da Jihar Borno ke ciki

- Zulum ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadan Falasdinawa a fadar gwamnatin jihar Borno

- A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar

Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

"Ni mutum ne mai son yin abu a aikace. Ina amfani da zahirin abinda na gani a ƙasa.

"Cikin shekarun da muke fama da ƙalubale, mun karɓi tallafi daga UK da wasu ƙasashen Turai da US, Canada har daga Japan da suka nuna damuwarsu wajen tallafawa da magunguna da kayan abinci"

"Larabawa ba su taɓa nuna damuwarsu gare mu ba. Ziyarar ka ta Ba mu kwarin gwiwa kan ku, muna matuƙar godiya" in ji Zulum.

KARANTA: Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

Ambasadan na Falasɗinu ya sanar da Zulum da wani shirinsu na tallafawa Jihar Borno a inda suke da buƙata.

Kasashen Turai sun fi tausayi da taimakon jihar Borno a kan kasashen Larabawa
Kasashen Turai sun fi tausayi da taimakon jihar Borno a kan kasashen Larabawa @Vanguard
Source: Twitter

"Akwai kamfanonin Falasɗinawa da yawa a Najeriya da suke son aiki da gwamnatin Borno, a shirye muke da haɗin gwiwa da ku, a shirye muke da mu tallafe ku da duk abinda kuke son wanda za mu iya."

Ambasadan ya kara da cewa, akwai da yawa yan Najeriya ciki har da yan asalin Borno da ke zaune a Falasɗin har ma suke shiga gwamnati ake damawa da su.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito Zulum na cewa duk da karuwar hare-haren mayakan Boko Haram, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda jaridu suka rawaito.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel