London Clinic: Abubuwan Mamaki game da Asibitin da Muhammadu Buhari Ya Rasu
- Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu a asibitin London Clinic inda ya shafe kwanaki 230 yana jinya tun lokacin mulkinsa har zuwa rasuwarsa
- Asibitin da Buhari ke jinya yana da tarihin karɓar manyan shugabanni da sarakuna, ciki har da ‘yan siyasa da sarakunan Birtaniya
- A cikin wannan rahoton, mun kawo muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da asibitin, ciki har da zarge-zargen da ake yi masa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
London - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu a ranar Lahadi a asibitin 'London Clinic' da ke Marylebone, kasar Ingila.
Ya shafe kwanaki 230 yana karɓar magani a can a tsawon shekaru takwas na mulkinsa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Source: Twitter
Asibitin, wanda ke lamba 22 Devonshire Place, Landan, babban asibiti ne mai zaman kansa wanda ke karɓar shugabannin siyasa, mashahuran masu kuɗi da kuma majinyatan diflomasiyya, inji rahoton FIJ.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FIJ gidauniya ce da ke tallafawa 'yan jarida masu binciken kwakwaf, kuma an wallafa wannan rahoton a shafin gidauniyar a ranar 14 ga Yulin 2025.
Rashin lafiyar Buhari da jinyarsa
A lokuta da dama a tsawon mulkinsa na shekaru takwas, tsohon janar din mai shekaru 82 ya mayar da Ingila ta zama cibiyar kula da lafiyarsa.
Bai taɓa bayyana musabbabin rashin lafiyarsa ko sunan cibiyar kiwon lafiyar da yake jinya ga jama'a ba. An kula da al'amuran lafiyarsa cikin sirri sosai.
Ko bayan barin mulki, ziyararsa ta lafiya zuwa ƙasar ba ta tsaya ba.
Bayan zarge-zargen kafofin watsa labarai game da lafiyarsa, tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Garba Shehu ya ce Buhari na samun sauki a asibitin na Landan.
Amma jaridar Sahara Reporters ta rahoto cewa Muhammadu Buhari ya rasu ne sanadiyyar cutar kansar jini, amma babu hujja a game da wannan.
Kasancewar shi ne wurin da ya rasu, da kuma yadda mataimakansa ke ci gaba da sanarwa a lokacin mulkinsa cewa yana ziyartar Landan don neman magani, akwai alamomi masu ƙarfi cewa wannan asibitin ne ya kasance yana ziyarta don samun kulawar likitoci yayin da yake mulkin Najeriya.
Shahararrun majinyatan asibitin London Clinic
Fitattun 'yan siyasa da ma sarakuna, ciki har da 'yan masarautar Birtaniya, a faɗin duniya sun sami kulawa a wannan cibiyar, inji rahoton jaridar Independent da ke Landan.
Shugabannin siyasa kamar tsohon shugaban Amurka John F Kennedy, tsoffin firaministocin Burtaniya Clement Attlee da Sir Anthony Eden sun kasance majinyata a asibitin.
Cecil Parkinson, wani fitaccen ɗan siyasa na Birtaniya, ya rasu sanadiyyar cutar daji ta hanji a asibitin a 2016. A 1966 asibitin ya karbi haihuwar David Cameron, wani tsohon shugaban Birtaniya.
A 1998, Augusto Pinochet, tsohon shugaban ƙasar Chile, ya samu kulawar likitocin asibitin a lokacin da aka kama shi saboda laifuffukan cin zarafin bil'adama.
Wasu daga cikin manyan sarakunan Birtaniya da suka ziyarci asibitin sun haɗa da tsohon Duke na Edinburgh, Prince Philip (mijin marigayiya Sarauniya Elizabeth) da kuma ƙanwar sarauniyar, Princess Margaret.
Mun ruwaito cewa, Sarki Charles III ma yana samun kulawar likitocin wannan asibitin a duk lokacin da ya kamu da rashin lafiya.
Binciken badakala da ta mamaye asibitin
Kwanan nan, an binciki asibitin kan wani lamari na fitar da sirrukan majinya ba bisa ka'ida ba, kamar yadda rahoton ABC News ya nuna.
A watan Janairu, aka yi wa Kate Middleton, Gimbiyar Wales ta Birtaniya tiyatar ciki a can. Jim kaɗan bayan sallamarta, aka ruwaito cewa wasu ma'aikatan asibitin sun sami damar shiga bayanan lafiyarta ba bisa ƙa'ida ba.
An ce wannan ya sanya hukumar kula da bayanan sirri (ICO), mai kula da bayanan Birtaniya, ta fara bincike kan wannan lamari.
A shafin yanar gizo na kungiyar asibitoci masu zaman kansu (IHPN), asibitin London Clinic ya wallafa cewa:
"Mu ne asibiti mai zaman kansa mafi girma a Birtaniya, muna kula da majinyata 195,000 a shekara".
Manyan ayyukan da asibitin ke gudanarwa
Asabitin ya kuma nuna alfahari da ƙwarewa a cikin manyan hanyoyin magani kamar su ilimin cutar kansa da gurbacewar jini, gyaran kashi, ciki har da tiyatar kashin baya.
Sauran bangarorin da asibitin ya kware a kansu sun hada da, cutar 'yan hanji, tiyata kowace iri, ciwon ido, ENT, tiyatar kwakwalwa, tiyata ta amfani da na'ura mai sarrafa kansa, tiyata mai ƙarancin shiga jiki da kuma kulawar lafiya mai zurfi.
Yana da manyan dakunan aiki guda bakwai da dakunan kulawa guda shida don tiyatar ƙirji, kashin baya, mafitsara, mahaifa da kasusuwas.
La'akari da tarihin asibitin na kula da manyan majinyata a duk duniya tun lokacin da aka kafa shi a 1932, ba abin mamaki bane Buhari ya sanya shi zama wurin da ya fi so don bukatunsa na lafiya. Yana da shekaru 11 kacal lokacin da aka buɗe asibitin.

Source: Twitter
Lokutan ziyarar Buhari zuwa asibitin
Buhari ya shafe aƙalla kwanaki 230 yana hutun jinya a lokacin da yake kan mulki, a cewar wani rahoto na ICIR.
A watan Fabrairun 2016, ya tafi Birtaniya saboda dalilai na lafiya kuma a watan Yuni na shekarar ya sake komawa don duba lafiyar kunnensa.
Ya sake tafiya Birtaniya a Janairun 2017 inda ya shafe tsawon kwanaki 50. Jim kaɗan bayan haka, ya sanar da wata tafiya da ta kai shi kwanaki 104 kafin ya dawo don ci gaba da mulki.
Ya ziyarci Birtaniya a watan Mayun 2018, Maris na 2021, Maris da Oktoba na 2022, wanda ya sa kasar ta zama wurin duba lafiyarsa.
A ƙarshen mulkinsa, ya ziyarci Birtaniya don dalilai guda biyu: don halartar bikin nadin sarautar Charles da kuma tiyatar haƙori.
Ana so Tinubu ya gyara asibitocin Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban lauya, Deji Adeyanju, ya nemi Shugaba Bola Tinubu ya gina asibitoci da za su dace da kiwon lafiya na duniya.
Ya ce Najeriya na bukatar asibitin zamani don dakile dogaro da kasashen waje, bayan rasuwar Muhammadu Buhari a asibitin London.
Adeyanju ya jaddada cewa aikin yana yiwuwa kafin karshen wa’adin mulkin Tinubu, idan aka nuna jajircewa da kudurin siyasa mai karfi .
Asali: Legit.ng




