Farfesan jami’a ya gano sabbin magunguna cutar Kansa da tarin fuka masu inganci

Farfesan jami’a ya gano sabbin magunguna cutar Kansa da tarin fuka masu inganci

Wani babban malamin jami’a, Farfesa Joshuwa Obaleye na sashin ilimin sinadarai Chemistry a jami’ar Ilorin ya kirkiro wasu sabbin magungun cutar kansa, zazzabin cizon saurao da kuma tarin fuka, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Obaleye ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Ilorin, inda yace sun gudanar da gwaje gwajen sinadarai a dakin bincikensa, kuma bincikensu ya nuna idan aka hada sinadarin karfe a cikin magungun yana kara musu karfi da inganci.

KU KARANTA: Wata shari’ar sai a lahira: Yadda Boko Haram ke daura ‘aure kan aure’

Obaleye, wanda shine shugaban kungiyar America Chemical Society reshen Najeriya, kuma shine shugaban Nigeria Chemical Society reshen jahar Kwara ya bayyana cewa matsalarsa daya bayan gano wadannan magungunan shine rashin kudin da zai hadasu dayawa ya shigar dasu kasuwa.

“Muna bukatar shigar da magungunan kasuwa, don haka muna gayyatar hukumar kula da ingancin abinci, NAFDAC da sauran hukumomi masu sa ido dasu zo su duba abinda muke yi don mu samu amincewarsu.” Inji shi.

Farfesan yace suna aiki tare da kwararrun masu binciken magunguna da masu hada magunguna daga kasashen India, Malaysia da Japan wajen gudanar da bincike, kuma yace ana samun nasara sosai da sosai.

Daga karshe Farfesan ya nemi gwamnatin tarayya ta taimaka masa da kudi don ganin an fitar da magungunan zuwa kasuwannin Najeriya dama duniya gaba daya domin a ceci rayuwar jama’a da dama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel