Yanzu-yanzu: Yarima Philip, mijin Sarauniyar Ingila ya riga mu gidan gaskiya
- Duke na Edinburgh, Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila Elizabeth II ya mutu
- A kwanakin baya an yi masa tiyata a zuciya aka sallamo shi a watan Maris
- Ya rasu ne a yau Juma'a a fadar Windsor kamar yadda gidan sarautar ta sanar
Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila Elizabeth na II ya rasu yana da shekaru 99 a duniya kamar yadda fadar Buckingham Palace ta sanar a ranar Juma'a.
An wallafa sanarwar rasuwarsa ne a shafin Twitter na fadar sarautar Ingila @RoyalFamily.
DUBA WANNAN: Jerin hamshaƙan mata 7 mafi arziki a duniya a shekarar 2021 da hotunansu
"Cikin tsananin jimami Mai Martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da rasuwar mijinta abin kaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburg," a cewar sanarwar.
"Mai martaba ya rasu ne a safiyar yau Juma'a a Fadar Windsor.
"Iyalan gidan sarauta na alhinin rasuwarsa tare da dukkan mutane a fadin duniya.
"Za a fitar da karin bayani a nan gaba."
Duke na Edinburgh, wanda ya shafe shekaru 73 yana auren Sarauniya Elizabeth ya ja baya daga ayyukansa na yi wa mutane hidima a shekarar 2017.
Shine basarake da ya fi dadewa kan karagar mulki a tarihin kasar Ingila.
KU KARANTA: Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya ta yanke su bayan kimanin shekaru 30
A watan Fabrairu an kwantar da shi a asibitin Sarki Edward VII da ke Central Landan bayan an sanar da cewa 'baya jin dadi'.
Duk da cewa fadar ta ce rashin lafiyansa bata da alaka da cutar COVID-19, ba a sanar wa duniya ainihin abin da ke damunsa ba.
Bayan an yi masa aikin zuciya a asibitin St Bartholomew's a Landan, an sallame shi a watan Maris.
Philip sun haifi yara hudu tare da sarauniya Elizabeth, sunayensu Yarima Charles, Gimbiya Anne, Yarima Andrew da Yarima Edward.
Asali: Legit.ng