Isra'ila da Iran Sun Amince Su Tsagaita Wuta, Shugaban Amurka Ya Fitar da Sanarwa

Isra'ila da Iran Sun Amince Su Tsagaita Wuta, Shugaban Amurka Ya Fitar da Sanarwa

  • Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa Isra'ila da Iran sun amince su tsagaita wuta bayan shafe kwanaki ana ɓarin wuta
  • Wannan kalamai na Trump na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan Iran ta kai harin ramuwar gayya kan sansanin sojin Amurka da ke kasar Qatar
  • Shugaba Trump ya ce alamu sun nuna yaƙin Iran da Isra'ila na iya shafe shekaru kuma ya tarwatsa yankin Larabawa, yana mai cewa hakan ba za ta faru ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

USA - Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen Iran da Isra’ila.

Shugaba Trump ya ce hakan ya kawo ƙarshen musayar wutar da aka shafe kusan kwanaki 12 ana yi tsakanin ƙasashen biyu, waɗanda suka jima suna takun saƙa.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta amince da tsagaita wuta, ta gargadi Iran kan kai mata hari

Shugaban Amurka ya ce za a tsagaita wuta.
Donald Trum ya sanar da cewa Isra'ila da Iran sun amince su tsagaita wuta Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Donald Trump ya sanar da cewa Isra'ila da Iran sun amince su tsagaita wuta ne a shafinsa na Truth Trump Social, wanda ke dandalin sada zumunta na X watau Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isra'ila da Iran sun amince su tsagaita wuta

A sanarwar da ya wallafa a daren ranar Litinin, 23 ga watan Yuni, 2025, Shugaba Trump ya taya kasashen murna bisa amincewa da wannan mataki na tagaita wuta.

"Ina taya kowa da kowa murna, Iran da Isra'ila sun amince su tsagaita wuta a tsakaninsu wanda zai fara aiki daga zuwa sa'o'i shida masu zuwa.
"Kuma nan da awanni 12, za a kawo ƙarshen wannan yaƙi tsakanin Isra'ia da Iran gaba ɗaya."

- Donald Trump.

Trump ya faɗi shirin kawo ƙarshen wannan yaƙi

Ya ƙara da cewa wannan yaki ne da "zai iya ɗaukar shekaru masu yawa, ya tarwatsa yankin Gabas ta Tsakiya", amma a cewarsa, hakan "ba zai faru ba, kuma ba zai faru ba har abada."

Kara karanta wannan

Iran ta kashe mutane a harin karshe zuwa Isra'ila, ta yaba da jarumtar sojojinta

Sai dai har zuwa yanzu, ba a samu wata sanarwa ko martani daga hukumomin Isra’ila ko Iran ba, wanda za ta tabbatar da wannan ikirari na Donald Trump.

Yakin tsakanin Iran da Isra’ila ya yi tsananin gaske a ‘yan makonnin da suka gabata, inda bangarorin biyu ke ci gaba da kai farmaki da martani a juna.

Firaminiatan Isra'ila da jagoran addinin musulunci na Iran.
Trump ya ce ba za a bari yaki ya kassara yankin Gabas ta Tsakiya ba Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shin Isra'ila da Iran sun amince da tsagaita wuta?

Tsagaita wutar da Trump ya sanar na iya zama mataki mai muhimmanci na samar da zaman lafiya, duk da babu tabbacin ko bangarorin biyu sun amince da hakan har kawo yanzu.

A tarihi dai Shugaban Amurka ya saba shiga tsakani don samun masalaha tsakanin Isra'ila da ƙasashen musulmi musamman a yankin Gabas ta Tsaliya.

A yanzu za a yi dakon jin ta bakin hukumomin Isra'ila da na Iran game da wannan batu na tsagaita, wanda ake sa ran zai kawo ƙarshen musayar wuta tsakanin ƙasashen biyu.

Trump ya yi magana kan ramuwar da Iran ta yi

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya ce harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar bai yi wano tasiri ba

Kara karanta wannan

Trump ya magantu kan sauya gwamnatin Iran, ya faɗi abin da zai tilasta faruwar haka

Shugaban Amurka ya ce sun samu sanarwa daga Iran kan batun kai harin, wanda ya ba su damar kwashe gaba ɗaya mutanen da ke wurin don gudun rasa rayuka.

Trump ya bayyana harin da Iran ta kai a matsayin mai rauni, yana mai cewa Amurka ba za ta tsaya ɓata lokacinta wajen rama wa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262