Shugaba Trump Ya Maida Martani bayan Iran Ta Kai Hari kan Sansanin Sojin Amurka

Shugaba Trump Ya Maida Martani bayan Iran Ta Kai Hari kan Sansanin Sojin Amurka

  • Donald Trump ya yi ikirarin cewa sun samu labarin Iran za ta kai farmaki sansanin sojin Amurka na Qatar tun kafin ta harba makamai
  • Trump ya ce wannan sanarwa da suka samu ta taimaka wajen kwashe duk wani ba Amurke daga wurin, don kaucewa asarar rayuka
  • Ya godewa Iran bisa ba su bayanai tun wuri, inda ya yi fatan cewa Jamhuriyar musuluncin za ta hakura, ta rungumi hanyar zaman lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United States, USA -Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, a ranar Litinin ya yi fatali da harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan wani sansanin sojin Amurka da ke Qatar.

Shugaba Trump ya bayyana harin da Iran ta kai a matsayin mai rauni, yana mai cewa Amurka ba za ta tsaya ɓata lokacinta wajen rama wa ba.

Kara karanta wannan

Iran ta kashe mutane a harin karshe zuwa Isra'ila, ta yaba da jarumtar sojojinta

Donald Trump, shugaban Amurka.
Sshugaban Amurka ya ce yana fatan Iran ta rungumi hanyar zaman lafiya Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Donald Trump ya faɗi haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, jim kaɗan bayan Iran ta harɓa makamai masu linzami kan sansanin sojin.Amurka na Al Udeid da ke ƙasar Qatar.

Wannan sansani dai yana ɗaya daga cikin manyan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya yi magana kan harin Iran a Qatar

Trump ya bayyana cewa Iran ta sanar da Amurka za ta kai harin tun kafin ta harba makamai zuwa sansanin sojojin kasar na Al Udeid Air Base da ke cikin Qatar.

"Ina farin cikin sanar da cewa babu ɗan Amurka da ya ji rauni, kuma kusan babu wata babbar barna da aka yi.
"Abu mafi muhimmanci shi ne sun fitar da fushinsu gaba ɗaya, kuma ina fatan hakan zai zama karshen duk wata gaba."

- Donald Trump.

Shugaban Amurka ya yi magana kan harin da aka kai Qatar.
Shugaba Donal Trump ya ce Amurka ba za ta maida martani ga Iran ba Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban Amurka ya godewa ƙasar Iran

Trump ya ƙara da godiya ga Iran saboda bayar da sanarwar gaggawa kafin kai harin, wanda ya bai wa Amurka damar kawo daƙile harin ba tare da an rasa rai ko samun rauni ba.

Kara karanta wannan

Trump ya magantu kan sauya gwamnatin Iran, ya faɗi abin da zai tilasta faruwar haka

“Ina so in gode wa Iran saboda sanarwar da suka bayar kafin lokaci, wadda ta sa babu wanda ya rasa rai ko ya ji rauni.
"Wataƙila yanzu Iran za ta yarda ta dawo neman zaman lafiya da jituwa a yankin, kuma zan marawa Isra’ila baya su ma su bi wannan hanya," in ji Trump.

Trump ya ƙara da cewa harin ramuwa da Iran ta kai bai yi muni ba, yana nuni da cewa Amurka ba za ta maida martani ba, domin a cewarsa, lamarin ya nuna babu ƙudurin yaki daga bangaren Iran.

Qatar da kakkaɓo makaman Iran

A wani labarin, kun ji cewa Qatar ta bayyana cewa na'urorin tsaron sama sun yi nasarar daƙile makamin da Iran ta harbo kan sansanin sojin Amurka na Al Udeid.

Ma’aikatar Tsaron Qatar ta sanar da cewa babu wanda ya samu rauni ko ya rasa rai sakamakon harin wanda Iran ta kaddamar ranar Litinin.

Wannan ma zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƙasar Amurka ta kai hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262