Jirgin Sama Ɗauke da Alhazai daga Saudiyya Ya Gamu da Matsala, Ana Zargin An Dasa Bam

Jirgin Sama Ɗauke da Alhazai daga Saudiyya Ya Gamu da Matsala, Ana Zargin An Dasa Bam

  • Wani jirgin sama da ya ɗauko alhazai daga ƙasar Saudiyya ya sauya akala, ya sauka a wani fili daban da wanda aka tsara masa a Indonesia
  • Hukumomin Indonesia sun ce an sauya wa jirgin wurin da ya sauka ne bayan samun sakon imel na barazanar dasa bam a cikin jirgin saman
  • Rahotanni sun nuna cewa an kwashe duka alhazan da ke cikin jirgin yayin da jami'ai ke ci gaba da bincike don gano na'urar bam

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Indonesia - Wani jirgin sama da ya ɗauko alhazai daga kasar Saudiyya ya gamu da tangarɗa yayin da ya zo sauka a ƙasar Indonesia.

Hukumomin sufurin jiragen sama na Indonesia sun tabbatar da cewa jirgin sama ɗauke da ɗaruruwan mahajjata daga Saudiyya ya sauka cikin gaggawa.

Alhazai sun gamu da cikas a Indonesia.
Jirgin da ya ɗauko alhazai ya yi saukat gaggawa bayan samun barazanar bam a Indonesia Hoto: Inside The Haramain
Source: Getty Images

A cewarsu, an sauya wa jirgin filin da zai sauka, daban da inda ya nufa, bayan da aka samu barazanar cewa an dasa bam a cikinsa, cewar rahoton Saudi Gazette.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Halin da Musulmin Iran ke ciki bayan luguden wutar Isra'ila a Tehran

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne wata sanarwa da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Indonesia (DGCA) ta fitar, ta ce an samu sakon barazanar bam din ne ta imel.

Jirgi ɗauke alhazai ya gamu da barazana

Hukumar ta bayyana cewa ta samu rahoto daga ma'aikatan filin jirgi game da sakon imel da wani ba a san ko wanene ba ya aiko, yana barazanar tayar da bam a jirgin.

“Sakon imel da aka samu da misalin ƙarfe 7:30 na safe (0030 GMT) ya ƙunshi barazana cewa za a tashi jirgin Saudia Airlines SV 5276,” in ji sanarwar.

Jirgin dai ya taso ne daga birnin Jeddah na Saudiyya zuwa filin jirgin Soekarno-Hatta na birnin Jakarta na kasar Indonesia.

Matukin jirgin ya sauya wurin sauka

Amma da misalin ƙarfe 10:00 na safe, matuƙan jirgin suka yanke shawarar karkatar da shi zuwa filin jirgin Kualanamu da ke Medan, wani birni a tsibirin Sumatra.

Jirgin saman dai yana ɗauke da mahajjata 442, ciki har da mazaje 207 da mata 235, waɗanda suka kammala aikin hajji kwana nan.

Kara karanta wannan

Jirgin sama ya sake faduwa a kasar India, an rasa rayukan mutane 7 sun riga mu gidan gaskiya

“Sakamakon barazanar tsaro, matukin jirgin ya yanke shawarar sauka wani filin jirgin sama mafi kusa da wannan don kare lafiyar fasinjoji,”

- inji kamfanin jirgin InJourney.

Jirgin sam ya gamu da tangarɗa.
An sauya wurin saukar jirgin alhazai bayan samun barazanar bam a Indonesia Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Wani jami’i daga ma’aikatar sufuri ya shaida wa manema labarai cewa har yanzu jirgin yana Medan, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Tuni dai ma'aikata suka sauke alhazan cikin tsaro, yayin da ƙwararru a fannin kwance bam ke ci gaba da gudanar da bincike don gano wanda aka dasa a jirgin.

Yadda aka hana mutane 200,000 hajjin 2025

A wani rahoton, kun ji cewa hukumomin Saudiyya sun hana dubban mutane sauke farali a lokacin aikin hajjin bana, 2025.

Saudiyya ta bayyana cewa wadanda aka dakatar sun yi yunkurin shiga kasar ba tare da izinin shiga ba, kuma wannan wani mataki na dakile shigar da maniyyata ba bisa doka ba.

Doka ta tanadi hukunci har zuwa tarar $5,000 da kuma fitar da mutum daga kasar ga duk wanda aka kama yana yunkurin aikin hajji ba tare da izini ba

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262