Jirgi Ya Rikito daga Sama Ya Fado cikin Gari, Gidaje 15 Sun Kama da Wuta

Jirgi Ya Rikito daga Sama Ya Fado cikin Gari, Gidaje 15 Sun Kama da Wuta

  • Wani jirgin sama kirar Cessna 550 Citation ya faɗo a cikin garin San Diego, lamarin da ya haddasa konewar gidaje 15 da motoci da dama
  • Hukumar kashe gobara ta ce ana bincike gida-gida domin tabbatar da cewa ba a bar kowa ciki ba, yayin da sojoji da jami'ai ke aikin ceto
  • An ce jirgin ya faɗo a lokacin da hazo ya lullube sararin samaniya, inda makwabtan unguwar suka ce fashewar ta girgiza gidajensu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Wani ƙaramin jirgin sama ya faɗo cikin wata unguwa da ke San Diego, Amurka, lamarin da ya jawo konewar akalla gidaje 15.

Jirgin kirar Cessna 550 Citation II ya faɗo ne da misalin ƙarfe 3:45 na safiyar Alhamis, a kusa da filin jirgin Montgomery-Gibbs Executive, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Kara karanta wannan

An fara raba tallafin gwamnatin Tinubu, mutane miliyan 15 za su ci gajiyar shirin

Ana fargabar mutum 1 ya mutu da jirgin sama ya fado kan gidajen mutane a San Diego
Yadda motoci suka kone kurmus bayan jirgin sama ya fado cikin San Diego. Hoto: SANDY HUFFAKER / Contributor
Source: Getty Images

Jirgin sama ya fado kan gidajen mutane

Rahoton BBC ya nuna cewa ana ci gaba da kwashe mutane daga gidajen da ke kusa da wurin da jirgin ya faɗo yayin da ake fargabar mutum daya ya mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ko suka mutu ba a hukumance ba, an ce akwai sansanonin sojoji a cikin unguwar da jirgin ya fada.

Dan Eddy, mataimakin shugaban hukumar kashe gobara na San Diego, ya ce:

“Akwai motoci da dama da wutar ta kone su sakamakon zubar fetur din jirgin a ko ina. Mun kira ƙungiyar kula da hadarin sinadarai, kuma muna aiki tare da sojoji.”

Ya ƙara da cewa:

“Babban abin da muke mayar da hankali a kai shi ne tabbatar da cewa ba a bar kowa a cikin gidajen da ke kusa da wurin ba. Daga nan za mu karasa inda jirgin ya faɗo, mu bincika."

Kara karanta wannan

Ayyuka 11,122 da ake zargin 'yan majalisar tarayya sun cusa a kasafin kudin 2025

Abin da ake zargin ya jawo fadowar jirgin

Mr. Eddy ya tabbatar da cewa jirgin ya yi karo da gidaje da dama a unguwar Murphy Canyon, inda ya bayyana cewa kayayyakin jirgin sun warwatse a wurare da dama.

Ya ce ana zargin yanayin hazo da ya yi karfi ne ya sa matukin jirgin ya rasa ikon jirgin har ya faɗo, domin “ba ka iya ganin gabanka.”

Eddy ya bayyana cewa wurin da jirgin ya fado ya zama kamar irin wanda 'yan fim ke hadawa, inda ya ce masu ceto na ci gaba da kokarin gano matukin jirgin da duk wanda ke ciki.

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta tarayya (FAA) ta ce ba a tabbatar da yawan mutanen da ke cikin jirgin ba, amma an ce jirgin Cessna 550 na iya ɗaukar fasinjoji 6 zuwa 8, ban da matuka jirgi biyu.

Jirgin sama da ya yi hatsari ya fado a San Diego ya jawo gidaje 15 sun kone
Wasu motoci da suka kone kurmus yayin da jirgin sama ya fado wata unguwa a San Diego. Hoto: SANDY HUFFAKER / Contributor
Source: Getty Images

San Diego: An ji halin da mutane suka shiga

Bidiyo daga wurin ya nuna gobara tana ci a gidaje da motoci, tare da tarin karikitan jirgi da motoci da tuni wuta ta ƙone su, sannan wani gida ya rushe sakamakon gobarar.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Gwamna ya rufe 'gidan karuwai' da ake baɗala a makarantar firamare

Mazauna unguwar sun shaida wa kafar labaran Sky News cewa sun ji “fashewa mai tsanani” sannan bangon gidajensu ya “girgiza.”

Christopher Moore, wanda ke zaune kusa da wurin da hatsarin jirgin ya faru, ya ce shi da matarsa sun farka sakamakon karar fashewar, sannan suka ga hayaƙi daga tagarsu.

Ya ce sun hazarta sun tattara kananun ‘ya’yansu biyu suka bar gidan, inda suka hango wata mota tana ci da wuta a lokacin da suke kokarin barin unguwar.

Jirgi ya fado kan gidajen mutane a Sudan

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu fararen hula da sojoji sun rasa rayukansu bayan jirgin yakin sojin Sudan ya faɗo kan gidaje a birnin Khartoum.

Hukumomin Sudan sun tabbatar da mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu da ke karɓar kulawa a asibiti bayan hadarin ya faru.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne sakamakon tangarɗar na’ura yayin da rundunar sojin Sudan ke ci gaba da artabu da dakarun RSF a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com