"Kun Wahalar da Alhazai, Gwamna Ya Ɗauki Zafi Yayin da Ya Yi Barazana ga NAHCON

"Kun Wahalar da Alhazai, Gwamna Ya Ɗauki Zafi Yayin da Ya Yi Barazana ga NAHCON

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya koka kan yadda alhazai suka tsinci kansu a Saudiyya a bana
  • Gwamnan ya soki tsarin hukumar NAHCON inda ya ce ya kamata a ba jihohi ragamar kula da alhazansu domin samar musu da walwala
  • Legit Hausa ta tattauna da wani mahajjaci daga jihar Gombe kan tsare-tsaren hukumar kula da alhazai ts NAHCON

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

Bala ya nuna damuwa kan yadda hukumar ta ba mahajjatan kunya a Saudiyya ganin yadda ta ke tafiyar lamarin a bana.

Gwamna ya soki tsarin NAHCON a bana, ya yi barazanar karbar ragamar kula jiharsa
Gwamna Bala Mohammed ya caccaki tsarin hukumar NAHCON a bana. Hoto: Senator Bala Mohammed.
Asali: Facebook

Bauchi: Bala ya koka kan tsare-tsaren NAHCON

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauki tsattsauran mataki kan masallatai da coci a Plateau, ya kakaba doka

Sanata Bala ya bayyana haka ne yayin zantawa da mahajjatan jihar Bauchi a Mina da ke Makkah a kasar, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya bukaci gyara kan ayyukan hukumar domin samun sauyi a yadda take gudanar da ayyukanta, kamar yadda Punch ta tattaro.

Har ila yau, gwamnan ya bukaci a bar gwamnatocin jihohi su na kula da alhazansu tun da ta jiha suke biyan kudin aikin hajji.

Ya bayyana damuwa kan yadda mahajjata suka fuskanci wahalhalu saboda tsare-tsaren hukumar da sauran masu ruwa da tsaki.

Gwamna Bala ya yi barazana ga NAHCON

Tsohon Ministan ya ba da misalin yadda hukumar ta ba alhazai dala 500 a matsayin alawus na tafiye-tafiye duk da N8m da suka karba a hannun alhazan.

Daga bisani, gwamnan ya ce zai hada kai da sauran gwamnoni domin kwace ikon hukumar idan ba ta sauya tsarin da take tafiya a kai ba.

Kara karanta wannan

Ba a gama da rigimar sarautar Kano ba, Gwamna ya yi dokar dakile tasirin sarakuna

Sanata Bala ya yi amfani da wannan dama inda ya ba alhazan jiharsa 2,689 riyal 300 kowannensu a matsayin goron sallah.

Tattaunawar wakilin Legit Hausa da wani Alhaji

Legit Hausa ta tattauna da wani mahajjaci daga jihar Gombe kan tsare-tsaren hukumar NAHCON

Alhaji Muhammad Abdullahi ya ce shi ba yau ya fara zuwa ba amma a gaskiya an samu matsaloli da dama.

"Kullum kara inganta abubuwa ake yi a Saudiyya amma bana an dan samu matsaloli musamman daga ɓangaren hukumar NAHCON."
"Musamman yawan mace-mace da aka samu duk da ƙaddara ne daga Allah kuma ba iya Najeriya ba ne."
"Na ji wasu gwamnoni suna korafi tare da kiran a basu kula da alhazansu, idan har za a bi tsari hakan ba matsala ba ne."

- Muhmmad Abdullahi

Abba ya ba mahajjata riyal 100

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya ba mahajjatan jihar Kano 3,121 goron sallah a kasar Saudiyya.

Abba ya ba kowane mahajjaci riyal 100 domin gudanar da Sallah cikin walwala yayin da suke kasa mai tsarki domin aikin hajji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.