Ma'aikata Na Kuka, Abba Kabir Ya Juya Kan Mahajjatan Kano 3,121 a Saudiyya

Ma'aikata Na Kuka, Abba Kabir Ya Juya Kan Mahajjatan Kano 3,121 a Saudiyya

  • Gwamnan jihart Kano, Abba Kabir ya sake ba mahajjatan jihar goron sallah yayin da suke kasar Saudiyya
  • Gwamnan ya ba mahajjatan 3,121 kyautar riyal 100 domin gudanar da shagulgulan bukuwan sallah
  • Mataimakin gwamnan jihar, Abdulsalam Gwarzo shi ya sanar da haka yayin ziyara sansanin 'yan jihar da ke kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake abin alheri ga maniyyatan jihar da ke kasar Saudiyya.

Abba Kabir ya gwangwaje mahajjatan da riyal 100 ga mahajjata 3,121 da suka fito daga fadin jihar baki daya.

Abba Kabir ya ba mahajjatan Kano kyautar makudan kudi
Abba Kabir ya ba mahajjatan Kano 3,121 goron sallah a Saudiyya. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Abba Kabir ya gwangwaje mahajjata

Mataimakin gwamman, Abdulsalam Aminu Gwarzo shi ya tabbatar da haka yayin ziyara sansanin mahajjatan da ke Mina a Saudiyya, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Kun wahalar da alhazai, Gwamna ya ɗauki zafi yayin da ya yi barazana ga NAHCON

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwarzo ya ce gwamnan a baya ya cikatawa mahajjatan N50,000 bayan kara kudin aikin hajji da kuma karin N150,000.

Mataimakin gwamnan ya bukaci mahajjatan da su dage da addu'a musamman domin samun zaman lafiya a kasar, cewar Punch.

Ya kuma bukace su da su kasance jakadu nagari a Saudiyya wurin kare martabar jihar da kuma Najeriya baki daya.

Kano: Gwarzo ya kai ziyara sansanin mahajjata

Daga bisani, Gwarzo ya kai ziyara duka sansanonin mahajjatan na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar a kasar Saudiyya.

Gwarzo ya samu rakiyar shugaban Majalisar jihar, Hon. Yusuf Jibrin Falgore da da sauran mambobin Majalisar.

Sannan daga cikin tawagar akwai shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Abdullahi Musa da shugaban hukumar alhazai a Kano, Alhaji Yusuf Lawal.

Sauran sun hada da babban darakta a hukumar alhazai, Alhaji Lamin Rabiu da kuma mataimakiyar kwamandan Hisbah ta bangaren mata, Dakta Khadija Sulaiman.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana hanyar da za a kawo ƙarshen tsadar rayuwa a Najeriya

Abba Kabir ya tallafawa maniyyata a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gwangwaje maniyyatan jihar Kano da kyautar N500,000.

Gwamna ya ba da kyautar domin ragewa mahajjatan halin da suke ciki a kasar musamman tsadar kujerar hajji a Najeriya.

Wannan kyauta na daga cikin tallafi da gwamnan ya bayar bayan karin kudin kujerar hajji da hukumar NAHCON ta yi a fadin Najeriya a bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.