Bitcoin: Muhimman Abubuwa 14 Game da Cryptocurrency a Shekarar 2024

Bitcoin: Muhimman Abubuwa 14 Game da Cryptocurrency a Shekarar 2024

Cryptocurrency wasu nau'in kudade ne na intanet wanda ake gudanar da kasuwancin su a tsarin sirrantawa na fasahar 'blockchain,' wanda Bitcoin ya zama jagora a sulallan.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A yayin da wasu ke kasuwancin kudin intanet domin samun riba, wasu kuma na amfani da fasahar ne kawai domin turawa da karbar kudi ba tare da an gane daga ina suke yin hakan ba.

Kasashe da dama ba su amince 'yan ƙasar su suyi kasuwancin crypto ba, kamar dai Najeriya.

Amma kasashe irin Indiya sun fara kirkirar na ta kudin intanet din domin ba su gamsu da wanda ake amfani da shi a yanzu ba.

Kara karanta wannan

"Jima'i kadai ke rage mana kunci": 'Yan gudun hijira sun cika sansani da jarirai

Kasuwar Cryptocurrency
Muhimman abubuwan da muka sani game da kasuwar Cryptocurrency. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, za mu duba amfanin kasuwancin cryptocurrency guda tara da kuma illolinsa guda biyar kamar yadda mujallar Forbes ta wallafa.

Amfanin kasuwancincryptocurrency

1. Kare hauhawar farashin kudi

Sakamakon hauhawar farashin kayayyaki kamar gwal, danyen mai da sauransu, darajar kudin kasashe da dama na faduwa a kasuwar duniya, in jir rahoton Economic Times.

Amma da zuwan fasahar kasuwancin kudi a intanet, an takaita faduwar sulallan da ke wakiltar kudi ko kayayyaki, kamar Bitcoin, NASDAQ, CRUDE OIL, USDT, da sauran su.

Idan aka ɗauki misalin Bitcoin, wanda ya zama jagora a kasuwar cryptocurrency, hawa da saukar farashinsa na shafar sauran sulalla da kuma farashin kayayyaki a duniya.

2. Sauri wajen hada hadar kudi

Idan har kana so ka tura kudi zuwa ga 'yan uwa da abokan arziki, misali a Amurka, to cryptocurrency na daga hanyar iya tura kudi komai yawansu cikin kankanin lokaci.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta DSTV da GOtv, ta umarci a haskawa 'yan Najeriya tashoshin kallo kyauta

Mutane sun rungumi kasuwar cryptocurrency saboda suna iya tura kudi cikin 'yan dakiku, sabanin banki da ke iya daukar kwana biyar.

3. Tura kudi daga 'kai' zuwa 'mai karba'

Ta hanyar cryptocurrency, za ka iya tura kudi zuwa kasashen duniya. Sau tari ba ka buƙatar biyan wani kamasho, wasu lokuta kuma za ka biya abin da bai taka kara ya karya ba.

Ba da damar tura kuɗi daga 'kai' zuwa 'mai karba' ba tare da wani ya tsoma baki ba, kamar banki da ke bukatar katin 'biza' ya karawa kasuwar daraja.

4. Babu mai iko da kasuwar crypto

Wani abu da ya sa mutane suka karbi kasuwar cryptocurrency shi ne kasancewarta mai zaman kanta, babu wani ko kungiya ko gwamnati da za ta yi iko da ita.

Babu wata gwamnati, kungiya ko mutane da za su iya kayyade darajar kudin na intanet, ko adadin yawan kudin da za a yi kasuwanci a rana, komai yana faruwa ne a kan tsarin jama'a.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta kama masu damfarar mutane domin sama musu izinin aikin hajji

5. Samun riba yayin hada-hadar kudi

Saka jari a kasuwar cryptocurrency yana ba da riba, kasuwar na ba da tarin damarmaki ga masu hada-hadar kudi a cikinta.

Duk da cewa ba a sami bayanan hada-hadar kudin gaba daya ba, amma dai an tabbatar tsarin samun kuɗi a crypto ya fi na Forex ko Stock.

Sai dai duk da irin ribar da ake samu, ita kasuwar cryptocurrency ba ta da tabbas, sulallan da ka siya na iya faduwa a daraja, dole ka yi zaman jiran farfadowar farashin.

6. Sauƙin mu'amala da kasuwar crypto

Masu zuba jari na bukatar na'ura mai ƙwaƙwalwa ko wayar hannu mai dauke da intanet domin shiga kasuwar cryptocurrency.

Ba a bukatar lallai sai ka saka bayanan ka, ko saka katin bankinka. Har sai idan za ka riƙa manyan hada-hadar kudi ne wasu dandalin kasuwar ke tantance masu jari.

7. Kasuwar cryptocurrency na da tsaro

Babu wanda zai iya shiga lalitar ka ta kasuwar cryptocurrency har ya saci kudi, sai dai idan kai ne ka yi sakaci har bayanan sirrinka suka fita waje.

Kara karanta wannan

Gwamnati na shirin janye harajin shigo da kaya, ana sa ran saukar farashin abinci

Haka zalika, akwai tsaro na karba da tura kudi wanda ake yin sa a tsarin fasahar blockchain, sai dai idan ka yi rashin sa'a ka tura kudi ga asusun da ba shi ba, za ka iya rasa kudin.

8. Babu hanyar zamba a kasuwar crypto

Kasancewar tsarin fasahar blockchain ba ta a karkashin ikon kowa, kana iya bibiyar kudin da ka tura ta hanyar amfani da manhajar blockchain din.

Wannan ya sa masu zuba jari suka kara gasgata kasuwar domin mai karba da mai turawa na iya sanin halin da kudin su ke ciki a lokacin hada-hadar.

9. Saukin musayar kuɗi a kasuwar

Masu saka hannun jari na iya siyan kudin na intanet ta hanyar amfani da kudin kasashe kamar dalar Amurka, rupee na Indiya ko Yuro na Europe.

Dandalin hada-hadar cryptocurrency daban-daban da suna taimaka wa masu saka hannun jari domin kasuwanci a cikin kasuwar crypto da musayar sulalla ba tare da an caje su kudi masu yawa ba.

Kara karanta wannan

An fallasa yadda gwamnonin jihohi suka kashe N960bn domin walwala a watanni 3

Menene rashin amfanin Cryptocurrency?

Zuba jari a cikin kasuwar cryptocurrency na iya zama mai ban sha'awa kuma mai riba amma akwai bukatar masu saka hannun jari su san matsalolin da ke tattare da kasuwar.

1 Ana gane masu kasuwancin Crypto

Ana ikirarin cewa Cryptocurrency nau'in ciniki ne wanda ake yinsa a sirran ce, amma a zahiri ba boyayyen kasuwanci ba ne, domin hukumar bincike ta FBI za ta iya gane masu yi.

Don haka, akwai yuwuwar tsoma baki daga hukumomin tarayya ko na gwamnati domin bin diddigin hada-hadar kudi na mutane na yau da kullun.

2. Akwai barazanar kutse ga kasuwar

A kan fasahar blockchain, akwai fargabar iya yin kutse ga masu hakar Bitcoin ko wasu sullalan crypto, ana ganin masu kutsen na da kaso 51 na damar kai wa kasuwar farmaki.

Idan an yi irin wannan farmakin, masu kutsen na daskarar da duk wata hada-hada da ake yi ta kai tsaye, su sauya adireshin tura kudi ko sulalla da kuma lalata adireshin daga baya.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

3. Amfani da wutar lantarki mai yawa

Yawancin blockchains suna aiki akan fasahar haɗin gwiwar shaida-na-aiki (POW). Ana buƙatar a yi amfani da na'urorin ASIC masu ƙarfi domin dora sabon adireshin 'block' a kan kasuwar.

Saboda haka, ana bukatar ayi amfani da wutar lantarki mai yawa wanda kuma ƙasashe da dama ke ɗaukar manyan matakai domin rage tasirin hakan ga muhalli.

4. Babu doka a kasuwar crypto

Rashin mahimman dokoki da suka danganci hada-hadar kudi ya zama babbar koma baya ga cryptocurrency. Hukumar SEC ta gargadi 'yan Najeriya kan crypto.

A yayin da wasu kasashen ke kokarin saka doka a kan kasuwar, wasu kuma sun yi dokoki domin haramta kasuwancin crypto.

5. Ana asarar kudi a kasuwar

A kasuwar crypto, idan har ka yi kuskuren tura kudi ga wani adireshi da ba shi kake son tura mawa ba, to sai dai ka dauki hakuri, domin ka rasa wannan kudin.

Kara karanta wannan

Masana sun fallasa yadda gwamnatin tarayya da dawo da tallafin man fetur a boye

Wata iriyar doka ce da dandalolin kasuwar crypto suka yi ta cewa mutum zai rasa kudinsa idan ya aikata kuskure wajen turawa, kuma babu wanda zai dawo masa da su.

Ka nemi ilimi kafin ka fara - Masani

Ko da muka tuntubi mai sharhi kan kasuwar crypto, Nura Haruna, daga kamfanin Deep Link Africa, ya gargadi 'yan Najeriya akan fara kasuwancin crypto ba tare da ilimi ba.

"Ya na daukar mutum tsawon shekaru yana koyon hada-hadar kudin crypto, amma ko ya kware a ilimin 'structure' da 'fundamental' na kasuwar, ba shi zai hana ya yi asara ba,
"To ina ga kuma wanda kawai zai shiga kasuwar yau, ya zuba kudi, kuma ya yi tunanin samun riba? Ai ka san wannan ganganci ne. Wannan ne ya sa mutane ke tafka asara a kasuwar."

Nura Haruna ya ce abu hudu ne za su taimaki mutum a kasuwar crypto; ilimi, hakuri, cire dogon buri da kuma jajurcewa.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata

Mansurah Isah ta yi sabon aure

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta yi wani sabon aure bayan shekaru uku da mutuwar aurenta.

A shekarar 2021 ne Mansurah Isah ta sanar da rabuwar ta da tsohon mijinta jarumi kuma mawaki Sani Danja. A mako biyu da suka gabata Mansura da Danja suka aurar da 'yar su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.