Ci gaba: Bayan haramta Bitcoin, CBN ta kirkiri amintattun kudaden Intanet na Najeriya
- Babban bankin Najeriya ya sanar da ranar da zai fara gwajin kudaden intanet da ya kirkira
- A baya babban bankin Najeriya ya haramta amfani da kudaden intanet, amma yanzu ya yi nashi da tsari
- Babban bankin ya bayyana yadda yake aikin kirkirar fasahar tun shekarar 2017 a can baya
Babban Bankin Najeriya ya ce zai kaddamar da tsarin gwajin kudinsa na intanet a ranar 1 ga Oktoba, 2021.
A cewar Nairametrics, CBN tare da masu ruwa da tsaki sun bayyana kudirin su na kudin intanet a wata ganarwar yanar gizo mai zaman kanta wacce aka gudanar a ranar Alhamis, 22 ga watan Yulin 2021.
A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar kwanan nan, Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin na aikin samar da kudin na intanet a yayin taron Kwamitin Banki na 306.
Nairametrics ta ce, majiyarta mai zaman kanta ta ce za a kaddamar da shirin ne a ranar 1 ga Oktoba, 2021.
Ta ce a jawabin da Daraktan sahen IT, Rakiya Mohammed ta yi a karshen taron ta bayyana cewa Bankin ya kasance yana gudanar da bincike a game da kudaden intanet na babban bankin tun shekarar 2017 kuma hakon kan iya cimma ruwa kafin karshen wannan shekarar.
Ana lakafta sunan aikin da Project GIANT kuma zai yi amfani da tsarin Blockchain na Hyperledger Fabric.
Kudin Intanet: Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta kasuwancin Bitcoin
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa bankunan Najeriya umarnin rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kudin yanar gizo na cryptocurrency, matakin da bai yi wa dubban 'yan Najeriya dadi ba, BBC Hausa ta ruwaito.
Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a ga bankunan hada-hadar kudi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kudi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kudi a kasar.
CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin
A wani labarin, Hukumar Tsaro da Musaya, babbar hukuma mai kula da kasuwar babban birnin kasar, ta ce za ta hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsari na yadda za a ke hada-hada da sauran kudaden intanet (Cryptocurrencies).
Darakta-Janar na SEC, Mista Lamido Yuguda, ya fadi haka a taron hadin gwiwa na kwamitin Majalisar Dattawa kan Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Manyan Kasuwanni da harkar fasahar sadarwa da Laifukan Intanet a Abuja, ranar Talata.
Babban Bankin na Najeriya a farkon wannan watan ya ba da umarni ga bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar da su rufe dukkan asusun kudaden intanet, The Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng