Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi

Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi

- Kasar Indiya ta bayyana kudurin haramta kudaden intanet a fadin kasar ba tare da bayyana dalili ba

- Kasar ta Indiya ta bayyana ba ta da wata matsala da fasahar kudaden intanet, amma ta kudurta haramcin

- Kasar China da wasu kasashe a shekarun bayan sun haramta kasuwacin irin wadanann kudaden

Gwamnatin Indiya ta yanke shawarar hana kasuwancin kudaden intanet da kuma cin tarar duk wani mai fatauci ko ya mallaki kudaden na intanet, Reuters ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran ya ambaci wani babban jami'in gwamnati wanda ba a bayyana sunansa ba da ke da masaniya kan kudurin, yana mai cewa kudirin zai hukunta mallaka, bayarwa, adana, kasuwanci da kuma musayar kudaden.

Jami'in ya ce kudurin zai bai wa masu rike da kudaden intanet har na tsawon watanni shida su cire kudadensu, bayan haka kuma za a zartar da hukunci.

KU KARANTA: Aure a muslunce: Mafi karancin sadakin aure ya haura Naira dubu 22 bana

Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi
Indiya za ta bi sahun Najeriya a harmata Bitcoin tare da garkame masu shi Hoto: Naira Metrics
Asali: UGC

A cewar jami'in, shirin gwamnati shi ne hana cinikayya masu zaman kansu yayin da suke tallata harkar blockchain - wata ingantacciyar hanyar fasahar bayanai wacce ita ce kashin bayan kudaden na intanet da masana suka ce na iya kawo sauyi ga ma'amalolin duniya.

“Ba mu da matsala da fasahar. Babu wata illa a cikin amfani da fasahar," jami'in yake cewa.

A shekarar 2019, kwamitin da gwamnatin Indiya ta kafa ya ba da shawarar hukuncin daurin shekaru 10 ga mutanen da suke hulda da kudaden intanet.

Jami'in ya ce tattaunawar tana matakin karshe amma ya ki ya bayyana ko wannan sabon kudirin ya hada da daurin rai da rai da kuma tara.

Idan haramcin ya zama doka, Indiya za ta kasance babbar kasa mai tattalin arziki na farko da ta sanya dokar haramci ga kudaden intanet.

China, Morocco da Iran kasashe ne da suka hana saye da sayarwa na kudaden intanet kamar su Bitcoin da Ethereum.

Babban Bankin Najeriya (CBN) kwanan nan ya umarci bankuna da sauran cibiyoyin kudi su rufe asusun mutanen da ke da hannun jari a kudaden intanet.

Babban bankin ya bukaci 'yan kasar da su daina amfani da kudin da ake kira crypto, yana mai gargadin cewa galibi ana amfani da su ne wajen daukar nauyin ayyuka laifi da suka sabawa doka.

KU KARANTA: Rundunar sojoji ta yi kicibus da 'yan Boko Haram, an yi rashin sojoji 3

A wani labarin daban, Hukumar Tsaro da Musaya, babbar hukuma mai kula da kasuwar babban birnin kasar, ta ce za ta hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsari na yadda za a ke hada-hada da sauran kudaden intanet (Cryptocurrencies).

Darakta-Janar na SEC, Mista Lamido Yuguda, ya fadi haka a taron hadin gwiwa na kwamitin Majalisar Dattawa kan Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Manyan Kasuwanni da harkar fasahar sadarwa da Laifukan Intanet a Abuja, ranar Talata.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel