Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

Abdurrassheed Bawa: Barayi suna amfani da Bitcoin wajen sace kudi a duniya

  • Shugaban hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa ya bayyana yadda kudaden intanet ke zama barazana ga kasashe
  • Ya bayyana cewa, ana amfani da Bitcoin da Ethereum wajen biyan kudin fansar hare-haren yanar gizo
  • Ya kuma jaddada cewa, lamarin ya shafi kasashe da dama, kuma yana kara ta'azzara har a kasashen da suka ci gaba

England - Abdulrasheed Bawa, shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ya ce kudaden intanet sun zama kyakkyawan zabi ga mutanen da ke gudanar da hada-hadar kudi ba bisa ka’ida ba, TheCable ta ruwaito.

Bawa ya fadi hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, a taron kasa da kasa na Cambridge karo na 38 kan laifukan tattalin arziki, mai taken, 'Laifin Tattalin Arziki: Wa Ya Biya kuma Wa Ya Kamata Ya Biya Farashi?'

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

Cibiyar Adana Bayanai ta Duniya kan Tsararrun Laifukan Tattalin Arziki (CIDOEC) a Kwalejin Jesus ta Jami'ar Cambridge a Burtaniya ce ta shirya taron.

Abdurrassheed Bawa: Barayi sun fi amfani da Bitcoin wajen sace kudi a Najeriya
Shugaban Hukumar EFCC, Mista Abdurrasheed Bawa | Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da Wilson Uwujaren, kakakin EFCC ya fitar, ya ambato Bawa na cewa amfani da kudaden intanet da 'yan ta'adda ke yi yana zama barazana ga tattalin arzikin duniya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Laifukan tattalin arziki, wadanda galibi haramtattun ayyuka ne da ake aikatawa don cin ribar kai, suna shafar mahimman tsarin tattalin arzikin duniya, suna haifar da babbar illa ga tsarin kudi na duniya da hana kasashe masu tasowa albarkatun da ake bukata don ci gaba mai dorewa."
"'Yan ta'adda a yanzu suna zabar yin hulda ko karbar haramtattun kudaden (kamar kudin fansa) na kai hare-hare ta yanar gizo ta hanyar kudaden intanet tare da Bitcoin da Ethereum a matsayin mafi yawan wadanda ake amfani dasu a wadannan musaya."

Kara karanta wannan

Festus Keyamo ya sha alwashin taimakawa wajen gano makasan dan uwan Sowore

Ya kuma ce kasashen da suka ci gaba su ma basu tsira daga irin wadannan matsaloli da suka saba wa doka ba, idan aka yi la’akari da “yaduwar laifuka ta yanar gizo wadanda ke zama barazana ga zaman lafiyar cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya”.

Ya kara da cewa

"Yayin da wadanda ake cuta ke ci gaba da shan wahala a duniya sakamakon illolin ta'addancin kudi, kai tsaye ko a kaikaice a matsayin wani bangare na tsarin zamantakewa, kudurin wanda ya biya ko wanda ya kamata ya biya farashi ya zama mahimmin ma'aunin tsarin shari'ar laifi a wurin

Ya kara da cewa shari’a ba tare da nuna bambanci ba zai zama mai mahimmanci wajen tabbatar da cewa “masu aikata ayyuka ba wadanda abin ya shafa suke biyan farashin laifukansu”.

Bayan haramta Bitcoin, CBN ta kirkiri amintattun kudaden Intanet na Najeriya

Babban Bankin Najeriya ya ce zai kaddamar da tsarin gwajin kudinsa na intanet a ranar 1 ga Oktoba, 2021.

Kara karanta wannan

Talauci: Rahoto ya nuna 'yan Najeriya miliyan 27 ke samun kudin shiga N100k a shekara

A cewar Nairametrics, CBN tare da masu ruwa da tsaki sun bayyana kudirin su na kudin intanet a wata ganarwar yanar gizo mai zaman kanta wacce aka gudanar a ranar Alhamis, 22 ga watan Yulin 2021.

A wani rahoto da jaridar Punch ta fitar kwanan nan, Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin na aikin samar da kudin na intanet a yayin taron Kwamitin Banki na 306.

Nairametrics ta ce, majiyarta mai zaman kanta ta ce za a kaddamar da shirin ne a ranar 1 ga Oktoba, 2021.

Ta ce a jawabin da Daraktan sahen IT, Rakiya Mohammed ta yi a karshen taron ta bayyana cewa Bankin ya kasance yana gudanar da bincike a game da kudaden intanet na babban bankin tun shekarar 2017 kuma hakon kan iya cimma ruwa kafin karshen wannan shekarar.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe mace mai juna biyu a Zaria

Ana lakafta sunan aikin da Project GIANT kuma zai yi amfani da tsarin Blockchain na Hyperledger Fabric.

CBN da wasu za su haɓaka tsarin gudanar da kasuwar Bitcoin

A wani labarin, Hukumar Tsaro da Musaya, babbar hukuma mai kula da kasuwar babban birnin kasar, ta ce za ta hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki don samar da tsari na yadda za a ke hada-hada da sauran kudaden intanet (Cryptocurrencies).

Darakta-Janar na SEC, Mista Lamido Yuguda, ya fadi haka a taron hadin gwiwa na kwamitin Majalisar Dattawa kan Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, Manyan Kasuwanni da harkar fasahar sadarwa da Laifukan Intanet a Abuja, ranar Talata.

Babban Bankin na Najeriya a farkon wannan watan ya ba da umarni ga bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar da su rufe dukkan asusun kudaden intanet, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya cilla kasar waje ziyarar aiki

Asali: Legit.ng

Online view pixel