Zaben Senegal: Dan Shekara 44, Bassirou Faye, Ya Kafa Tarihi a Siyasar Afrika
- A yayin da aka sanar da sakamakon zaben shugaban kasar Senegal, ɗan shekara 44, Bassirou Faye ya kafa tarihi a siyasar Afrika
- Rahotanni sun bayyana cewa Faye ya samu tazarar kuri'u mai yawa a zaben da aka gudanar a ranar Lahadi, yayin da Amadou Ba ke a baya
- Akalla ƴan takarar shugaban ƙasa guda shida cikin 19 suka taya Faye murna, yayin da aka nemi Ba ya amince da shan kaye a zaben
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Senegal - Dan siyasar Senegal mai shekaru 44, Bassirou Diomaye Faye, ya zama zababben shugaban kasa mafi karancin shekaru a nahiyar Afirka.
An taya Faye murnar cin zaben Senegal
A baya dai Daily Trust ta ruwaito cewa Faye wanda ke kan gaba a zaben kasar Senegal ya kasance daure a gidan yari kwanaki 10 gabanin zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akalla ‘yan takara shida daga cikin 19 ne suka fitar da sanarwar taya Faye murna tun da sanyin safiyar Litinin.
Da fari, babban abokin hamayyar Faye, Amadou Ba, daga jam’iyya mai mulki ya ce akwai yiwuwar a sake yin zaben domin gane wanda ya yi nasara.
"A namu bangaren, da kuma la'akari da martanin sakamakon da tawagar kwararrunmu suka bayar, muna da tabbacin cewa, za mu je zagaye na biyu a zaben."
- A cewar Ba, tsohon firaministan Senegal.
Ba ya taya Faye murnar lashe zabe
Amma yayin da tazarar Faye ke kara yawa, BBC ta ruwaito cewa Ba ya kira Faye a waya domin taya shi murnar lashe zaben kasar, wanda ke nufin ya amince da shan kaye a zaben.
Tazarar kuri'un da Faye ya samu ya zaburar da mabiyansa inda suka fito kwansu da kwarkwata a titunan babban birnin kasar da ke Dakar, ranar Lahadi domin nuna murna.
Rahotanni sun bayyana cewa miliyoyin mutane ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar Senegal na biyar bayan shafe shekaru uku ana rikicin siyasa da ba a taba ganin irinsa ba.
'Yan tsubbu za su yi wa Mane magani?
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta taɓa ruwaito maku cewa, ƙasar Senegal ta ce za ta yi amfani da malaman tsubbu wajen yi wa ɗan wasansu Sadio Mane magani.
Idan ba a manta ba, a baya Mane ya sha fama da rashin lafiya da har aka yi fargabar ba zai buga wasannin gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar ba.
Asali: Legit.ng