Kasar Senegal Na Neman Agajin Sojojin Najeriya Domin Yakar Rashin Tsaro

Kasar Senegal Na Neman Agajin Sojojin Najeriya Domin Yakar Rashin Tsaro

  • Rundunar sojojin kasar Senegal ta nemi hadin gwiwar sojojin Najeriya wajen yakar ta'addanci
  • Sojojin na Senegal sun bayyana cewa, sojojin Najeriya na da kwarewa da gogewa a fannoni da dama
  • Rundunar sojojin Najeriya ta yaba da neman hadin gwiwar kuma ta ce za ta yi mai yiwuwa wajen yakar ta'addanci

Sufeto-Janar na Sojojin Senegal, Maj.-Gen. Elhadji Niang, ya nemi hadin gwiwa da Sojojin Najeriya don magance matsalar ta'addanci a yankin Afirka da yankin Sahara, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mista Niang ya yi kiran ne a lokacin da ya kai wa Shugaban Hafsun Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor, ziyarar ban girma a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce ziyarar da ya kawo Najeriya ya zo ne da nufin duba irin shirin da jami'an tsaron Najeriya ke yi wadanda suka hada da sojojin kasa, ruwa da na sama da kuma ‘yan sanda.

KARANTA WANNAN: An Bindige Wani Dalibin Jami’a Bayan Rubuta Jarrabawarsa Ta Karshe a Jami’a

Kasar Senegal Na Neman Agajin Sojojin Najeriya Domin Yakar Rashin Tsaro
Shugaban Hafsun Tsaron Najeriya, Janar Lucky Irabor | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewarsa, babbar manufar ziyarar tasa ita ce bayyana sadaukarwar da sojojin Senegal suka yi na yin aiki kafada da kafada da sojojin Najeriya da nufin tunkarar kalubalen tayar da kayar baya da ta'addanci a yankin Afirka ta Yamma.

Ya ce:

“Mun yi imanin cewa yin aiki tare da Najeriya zai kara mana kwarin gwiwa saboda kwarewa da gogewar sojojin Najeriya a fannoni daban-daban.

"Muna fatan cewa daga wannan ziyarar za mu samo hanyoyin da za mu iya hada kai da kuma aiki sosai don magance matsalolinmu daban-daban."

Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Najeriya da Senegal, in ji Irabor

Da yake amsawa, CDS, Irabor, wanda ya yarda da cewa tsakanin Najeriya da Senegal akwai kyakkyawar dangantaka a matakan siyasa da kuma aikin soja.

Mista Irabor ya ce, kasashen biyu suna hulda da juna sosai ta fuskar aiki da horo, ya kara da cewa za a iya amfani da kwarewarsu don karin tasirin sojojin kasashen biyu.

A cewarsa, wannan shi ne dalilin da ya sa ya yi imanin cewa ziyarar shugaban sojojin na Senegal za ta ba sojojin kasashen biyu damar karfafa wannan dankon zumunci da suka yi.

Da yake amincewa da tayin hadin gwiwar, Irabor ya ce:

"Ina tsammanin hadin gwiwarmu zai taimaka wajen inganta yanayin rashin tsaro a yankin."

Babban Hafsan Sojoji Ya Kai Ziyara Imo, Ya Ce a Ragargaji IPOB Ba Sassautawa

Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin Najeriya, ya nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro yadda yake a jihar.

An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak.

KARANTA WANNAN:

Da Dumi-Dumi: Majalisar Wakilai Ta Tabbatar da Nadin Manjo Faruk Yahaya

A wani labarin daban, Majalisar wakilai ta tabbatar da Faruk Yahaya a matsayin shugaban hafsan soji (COAS).

Majalisar dokokin ta tabbatar da shi bayan gabatar da rahoto daga Babajimi Benson, shugaban kwamitin tsaro, The Cable ta ruwaito.

Idan baku manta ba, majalisar dattijai a ranar Talatar da ta gabata ne ta tabbatar da Yahaya a matsayin COAS.

Legit.ng Hausa ta gano cewa, yayin gabatar da rahoton, Benson ya ce Yahaya ya cika dukkan bukatun da ake fata daga gare shi. Ya ce shugaban sojojin ya amsa duk tambayoyin da kwamitin ya yi masa yayin bincike"yadda ya dace".

Asali: Legit.ng

Online view pixel