Shugaban Senegal Ya Soke Zaben Shugaban Kasa Awanni Kafin Fara Kamfe

Shugaban Senegal Ya Soke Zaben Shugaban Kasa Awanni Kafin Fara Kamfe

  • A karon farko an dage yin zaben shugaban kasa a Senegal biyo bayan wata doka da Shugaba Macky Sall ya rattabawa hannu
  • An shirya yin zaben shugaban kasar ne a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu kafin Shugaba Sall ya sanar da dagewar
  • Kamar yadda Shugaba Sall ya sanar a jawabinsa ya ce an dage yin zaben shugaban kasar ne saboda 'yan majalisa na bincikar wasu alkalan kundin tsarin mulki biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Senegal - Shugaban Senegal Macky Sall a ranar Asabar ya sanar da dage zaben shugaban kasa da aka shirya yi a ranar 25 ga watan Fabrairu har sai baba-ta-gani.

Shugaban kasar ya soke yin zaben ne 'yan awanni kafin fara yin yakin neman zabe a hukumance kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaba Macky Sall
An dage zaben shugaban kasa a Senegal 'yan awanni gabanin fara kamfe.
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki bayan kotu da datse dan PDP shiga takarar Sanata saura kwanaki 2 zabe

Menene dalilin soke zaben shugaban kasa a Senegal?

A cikin wani jawabi da ya yi wa kasar, Sall ya ce ya rattaba hannu kan dokar soke ranar fara zaben a baya saboda 'yan majalisa na bincikar wasu alkalan kundin tsarin mulki biyu da aka saka alamar tambaya game da gaskiyarsu.

Sali, ba tare da sanar da sabon ranar yin zaben ba ya kara da cewa:

"Zan fara tattaunawa ta kasa wacce za ta samar da yanayin gudanar da sahihin zabe na adalci ba tare da nuna son-kai ba."

An taba dage zaben shugaban kasa a Senegal?

Wannan ne karo na farko da aka fara dage zaben shugaban kasa a Senegal. Hakan na zuwa ne bayan rikici da ya barke tsakanin Majalisar Tarayya da Kotun Kundin Tsarin Mulki kan rashin amincewa da wasu 'yan takara.

Dokar da Sall ya saka wa hannu a Nuwamban 2023 ta ce za a yi zaben ne a ranar 25 ga watan Fabrairu inda akwai yan takara 20 amma an cire sunan manyan 'yan takara na jam'iyyun hamayya biyu.

Kara karanta wannan

An shiga rudani a Jos bayan Hukumar INEC ta cire sunan PDP a zaben cike gurbi, APC da LP sun shiga

Sall ya dade yana nanata cewa zai mika mulki a farkon watan Afrilu ga duk wanda ya lashe zabe, rahoton Reuters.

Bayan sanarwa cewa ba zai zarce karo na uku ba a matsayin shugaban kasa, Sall ya zabi Farai Minista Amadou Ba daga jam'iyyarsa a matsayin magajinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel