Kamar Buhari, Donald Trump Ya Fadi Mummunan Abin da Zai Faru Idan Bai Ci Zaben Amurka Ba

Kamar Buhari, Donald Trump Ya Fadi Mummunan Abin da Zai Faru Idan Bai Ci Zaben Amurka Ba

  • Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sha alwashin shiga kafar wando da kasar Sin a harkar kasuwanci
  • Trump ya bayyana haka ne yayin kamfe din ɗan takarar sanatan jam'iyyar Republican a yankin Ohio, Bernie Moreno
  • Ɗan takarar shugaban kasar ya ce za a zubar da jini kuma babu tabbacin sake zaɓe a Amurka idan bai ci zabe ba a kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Ohio, Amurka - Mai neman takarar shugaban kasa a Amurka, Donald Trump ya bayyana abin da zai faru idan bai ci zaben Nuwamba ba.

Tsohon shugaban kasar ya ce za a zubar da jini da kashe-kashe idan har ba a zabe shi ba a karo na biyu ba a matsayin shugaba Amurka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da sabon umarni ga rundunar tsaro bayan kisan sojoji 16, ya yi Allah wadai

Donald Trump ya gargadi Amurkawa da kan kin zabensa a matsayin shugaban kasa
Donald Trump ya ce za a zubar da jini idan ba a zabe shi a Amurka ba. Hoto: Donald Trump.
Asali: Facebook

Menene Trump ke cewa kan zaben Amurka?

Trump ya bayyana haka ne a Ohio yayin kamfe din ɗan takarar sanatan jam'iyyar Republican, Bernie Moreno, cewar France 24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da harkar kasuwanci mai tsauri da kasar Sin ba tare da daga musu kafa ba, cewar ABC News.

"Idan kuna ji, shugaban Sin da ni da ku abokai ne, amma ya san yadda nake, kamfanin motoci da suke kerawa a Mexico, za su hana Amurkawa aiki amma za su siyar mana, ba zai yiwu ba."
"Za mu saka musu haraji kaso 100 ga duk wata mota da ta zo, kuma ba za ku iya siyar da wadannan motocin ba idan na hau mulki."
"Idan ban ci zabe ba, za a zubar da jini a kasar, wannan mafi karanci kenan, idan ban ci zaben ba, ina tsammanin zai yi wahala a sake zabe a kasar nan."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

- Donald Trump

Trump: Martanin kakakin kamfen Shugaba Biden

A martanin kakakin kamfe na Trump, Karoline Leavitt ta ce tsare-tsaren Shugaba Biden za su lalata komai a kasar.

Yayin da James Singer, kakakin kamfe na Shugaba Biden ya ce Trump faɗaɗɗe ne madadin ya roki alfarmar kuri'u amma ya tsaya yana fatan samun rikicin siyasa.

Amurka ta haramtawa 'yan Najeriya shiga kasar

A baya, kun ji cewa Amurka ta dauki mataki a game da wasu ‘yan Najeriya da ake zargin su na neman kawowa damukaradiyya matsala.

Sakataren harkokin wajen kasar, Antony Blinken shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel